‘Adalcin shugabanni ne zai sa kasar nan ta zauna lafiya’

Sheikh Musa Aliyu Jahun shi ne malamin da yake  gabatar da tafsirin Al-kur’ani kowace shekara a Babban Masallacin Fanka Tara da ke unguwar Sabuwar Kasuwa Bauchi. Har ila yau,  shi ne  shugaban kwamitin da’awa na Jihar Bauchi. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya yi tsokaci game da muhimmancin kyautatawa marayu a watan azumi. Ga yadda tattaunawar […]

‘Adalcin shugabanni ne zai sa kasar nan ta zauna lafiya’
‘Adalcin shugabanni ne zai sa kasar nan ta zauna lafiya’

Sheikh Musa Aliyu Jahun shi ne malamin da yake  gabatar da tafsirin Al-kur’ani kowace shekara a Babban Masallacin Fanka Tara da ke unguwar Sabuwar Kasuwa Bauchi. Har ila yau,  shi ne  shugaban kwamitin da’awa na Jihar Bauchi. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya yi tsokaci game da muhimmancin kyautatawa marayu a watan azumi. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Farko za mu so ka gabatar dakanka?
Sheikh Musa: Dukkan godiya ta tabbatar ga Allah madaukacin sarki. Sunana Musa Aliyu Jahun mai gabatar da tafsiri a Masallacin Fanka Tara da ke Bauchi kuma ni ne shugaban kungiyar ci gaban matasan jahun.
Aminiya: Me ye sakonka ga shugabanni?
Sheikh Musa: Sakona a gareso shi ne kowa ya ga yadda aka yi da azzaluman shugabanni saboda haka yakamata duk wanda aka zabe shi ya dage sosai wajen shim fida ayyukan alheri ga mutanen mazabarsa domin bayan shekara hudu zai sake dawowa neman tazarce.
Kuma wannan kungiya ta “Jahun Awareness Forum” daya daga cikin manyan ayyukata shi kyautatawa marayu da marassa galihu kuma zamu ci gaba da ba da gudunmawa domin kyautata wa marasa galihu da ke tsakanin al’umma.
Don haka mun kafa wannan kungiya ne domin kyautata marayu da matan da mazajensu suka rasu.
Har ila yau, a matsayina na malamin addinin Musulunci zan ci gaba da ba da shawarwari mai amfani ga ’yan siyasa domin kowa ya gyara tafiyarsa. Muna kira da dababbar murya ga gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed Abubakar da ya tausaya wa al’umma domin fiye da kashi 55 cikin 100 na mutane basa iya cin abinci sau biyu a kullum.
Muna fatar alheri ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari Allah Ya ba shi ikon magance matsalolin ‘yan Najeriya wadanda suka kada masa kuri’a a zaben da ya gabata.
Aminiya: Me ye gaskiyar batun cewa wasu limamai sun nuna bacin ransu a kan rashin samun geron azumi?
Sheikh Musa: A matsayinana daya daga cikin limamai bani da masaniya game da wannan batu. Kuma bana ganin akwai wani limami da zai bata lokacinsa akan geron kunu da gwamnatin Jihar Bauchi take raba wa duk shekara. Geron kunu ba shi ne matsalar malaman jihar nan ba.
Muna fatar gwamnati za ta fadada wannan shiri na tallafawa masallatai a wannan wata na azumi. Ina rokon gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafawa marayu domin manzon Allah ya ce duk wanda ya taimaki maraya kafada da kafada za su shiga Aljannah da shi. Saboda haka muna fatar za a kyautatawa marayu da kayan sallah a wannan wata mai albarka.
Tabbas akwai wasu daga cikin malamai da ba su da wani aiki sai karban makudan kudade a wajen azzaluman shugabanni kowa ya ga yadda Allah Ya tona musu asiri a fili.
Aminiya: Me ye ra’ayinka game da kwamitin karbo kayayyakin gwamnati da aka kafa?
Sheikh Musa: Ina daya daga cikin malaman da suka fara nuna goyon bayansu da kafa kwamitin duk wanda ya dauki kayayyakin gwamnati muna fatan a bishi a karbo domin wannan zai zamo darasi na musamman ga ‘yan baya masu zuwa.
Aminiya: Me ye sakonka ga malamai ‘yan uwanka masu gabatar da tafsiri a masallatai?
Sheikh Musa: Babban sakona ga limamai shine ya kamata kowa ya ji tsoron Allah a karantar da mutane gaskiya da rikon amana. Kuma kada wani malami ya bari wani dan siyasa ya yi amfani da masallacinsa wajen kamfen. Babu wani malamin Allah da zai yadda ya tare a falon dan siyasa kowa ya kama sana’a domin ta haka ne mutum zai tsage gaskiya komai dacinsa.
Saboda haka ina tabbatar maka da cewa adalcin shugabanni ne zai sa Najeriya ta zauna lafiya kowa ya yi aikinsa ba tare da wata matsala ba.
Babu wata gwamnati da za ta samu ci gaba da kwanciyar hankali, sai ta yi adalci ga al’umma domin adalci shi ne sinadarin da ke kawo ci gaba a tsakanin al’umma.
Muna fatan wadanda aka zaba zasu iya bakin kokarinsu wajen kyautatawa al’umma domin za su sake dawowa a zabe mai zuwa.
Daga karshe muna fatan Allah Ya kawo zaman lafiya da kwanciyar a kasar nan domin babu wata al’umma da za ta samu ci gaba, sai da zaman lafiya.
Kuma a tuna da marayu domin suna cikin mawuyacin hali sakamakon karancin kudi a hannun al’umma.