Adali da mugu (3)
Hikimar mata takan gina gidaje, amma wauta takan rushe su. Ka yi gaskiya, za ka nuna girmamawarka ga Ubangiji, amma idan ka yi rashin gaskiya, ka nuna rashin girmamawa ke nan ga Ubangiji. Kalmomin mai hikima za su kiyaye shi, amma maganganun wawa za su jawo masa hukunci. Idan ba ka da shanun noma ba […]
Hikimar mata takan gina gidaje, amma wauta takan rushe su. Ka yi gaskiya, za ka nuna girmamawarka ga Ubangiji, amma idan ka yi rashin gaskiya, ka nuna rashin girmamawa ke nan ga Ubangiji. Kalmomin mai hikima za su kiyaye shi, amma maganganun wawa za su jawo masa hukunci. Idan ba ka da shanun noma ba za ka samu hatsi mai yawa ba, amma idan kana da su za ka samu hatsi mai yawan gaske. Amintaccen mashaidi a koyaushe yana fadar gaskiya, amma marar aminci ba ya fadar komai, sai karairayi. Mutum mai fariya ba zai taba zama mai hikima ba sam, amma mutum mai basira yakan koya a sawwake. Ka nisanci wawaye, gama ba su da abin da za su koya maka. Me ya sa haziki yake da hikima? Domin ya san abin da zai yi. Me ya sa dakiki yake da wauta? Domin yana ganin kansa masani ne. Idan wawaye sun yi zunubi ba sukan kula ba, amma mutanen kirki sukan nemi gafara. Bacin ranka naka ne, murnarka kuwa ba za ka raba da wani ba. Gidan mutumin kirki ba zai rushe ba bayan da an lalatar da gidan mugun mutum. Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka. Dariyar mutum takan boye bakin cikinsa. Sa’ar da murna ta tafi, koyaushe bakin ciki yana nan. Mugu zai samu abin da ya cancance shi, mutumin kirki kuma zai samu sakayyar ayyukansa. Wawa yakan gaskata kowane abu, amma mai la’akari yana lura da takawarsa. Mutum mai hankali yana lura don ya kauce wa wahala, amma wawa rashin kula gare shi, yakan aikata komai da gaggawa. Mutum mai zafin rai yakan yi aikin wauta, mai mugayen dabaru kuma abin ki ne. Jahilai sukan samu abin da ya cancanci wautarsu, amma ilimi shi ne sakamakon masu azanci. Tilas mugaye su rusuna wa adalai, su roke su tagomashi da tawali’u. Ba wanda yake son matalauci, amma attajiri yana da abokai da yawa. Idan kana so ka zama mai farin ciki, sai ka nuna alheri ga matalauci. Zunubi ne ka raina kowane mutum. Wadansu za su amince da kai, su girmama ka, idan ka aikata nagarta, idan kuwa ka aikata mugunta, to, ka yi babban kuskure. Idan ka yi aiki za ka samu abin masarufi, idan kuwa ka zauna kana ta surutu kawai za ka zama matalauci. Mutane masu hikima za a saka musu da wadata, amma za a san wawa ta wurin wautarsa. Sa’ar da mashaidi ya fadi gaskiya zai ceci rayuka, amma makaryacin mashaidi yakan ci amanar mutane sa’ar da ya fadi karairayi. Tsoron Ubangiji yakan ba da tabbatarwa, da zaman lafiya ga mutum da iyalinsa. Kana so ka kauce wa mutuwa? To, tsoron Ubangiji shi ne mabubbugar rai. Darajar sarki ta dogara ne ga irin yawan mutane da ya mallaka, idan babu su, shi ba komai ba ne. Mutum mai kamewa yana da hikima, amma mai zafin rai yana bayyana wautarsa a fili. Kwanciyar rai lafiya ce ga jiki, amma kishi yana kama da ciwon da yake cin kashi. Wanda ya zalunci matalauci ya zargi Mahaliccinsa ke nan, amma nuna alheri ga matalauci yin sujada ne. Muguntar mugun takan kawo hallakarsa, amma adalin mutum, an kiyaye shi ta wurin dattakunsa. Hikima tana cikin kowane tunani na haziki, wawa bai san komai game da hikima ba. Adalci yakan daukaka al’umma, amma zunubi yakan kunyatar da al’umma. Sarakuna suna jin dadin kwararrun ‘yan majalisarsu, amma sukan hukunta wadanda suka ba su kunya.
Amsa magana da tattausar harshe takan kwantar da hassala, amma magana da kakkausar harshe takan kuta fushi. Sa’ar da mai hikima ya yi magana yakan sa ilimi ya yi ban sha’awa, amma wawaye sukan yi ta sheka rashin hankali. Ubangiji Yana ganin abin da ke faruwa a ko’ina, yana lura da mu, ko muna aikata alheri ko mugunta. Kalmomin alheri suna kawo rai, amma maganganun kiyayya suna karya zuciyar mutum. Wauta ce mutum ya ki kulawa da abin da mahaifinsa ya koya masa, amma hikima ce idan ka karbi tsawatarwarsa. Adalai suna adana dukiyarsu, amma mugaye sukan rasa tasu dukiya sa’ar da wahala ta zo. Mutane masu hikima su ke yada ilimi, amma ban da wawaye. Ubangiji Yana murna sa’ar da adalai suke yin addu’a, amma Yana kin hadayun da mugaye suke mika maSa. Ubangiji Yana kin hanyoyin mugaye, amma Yana kaunar mutumin da ke yin abin da ke daidai. Idan ka yi abin da ba daidai ba, za ka sha hukunci sosai, za ka mutu idan ka ki yarda da tsawatarwa.
Ko Lahira ba za ta hana Ubangiji Ya san abin da ke can ba. Kaka fa mutum zai iya boye wa Allah tunaninsa? Mai girman kai ba ya so a tsawata masa. Faufau ba zai nemi shawara a wurin masu hikima ba. Sa’ar da mutum yake murna yakan yi murmushi, amma sa’ar da yake bakin ciki yakan yi nadama. Mutum mai basira yana neman ilimi, amma dakikai, jahilcinsu ya wadace su. Wahaltaccen mutum a koyaushe, fama yake yi a zamansa, amma masu farin ciki suna zama da dadin rai. Gara a zauna da talauci da tsoron Ubangiji, da a samu dukiya game da wahala. Gara cin mabunkusa tare da wadanda kake kauna, da ka ci abinci mai romo a inda kiyayya take. Zafin rai yakan kawo jayayya, amma hakuri yana kawo salama. Idan kai rago ne za ka gamu da wahala a ko’ina, amma idan kai amintacce ne, ba za ka sha wahala ba. Da mai hikima yana faranta zuciyar mahaifinsa, amma wawa yana raina mahaifiyarsa. Dakikai suna murna da wautarsu, amma mai hikima zai aikata abin da ke daidai. Ka nemi dukan shawarwarin da ka iya ka samu, za ka yi nasara, idan ba tare da shawara ba, za ka fadi. Me ya fi wannan zama abin murna? Mutum ya samu maganar da ke daidai a lokacin da ya dace! Mutum mai hikima yakan kama hanya ya haurawa zuwa rai, ba ya bin hanyar da ta gangara zuwa mutuwa.
(Karin Magana 14,15:1-24)