Adamu Aliero: Gwanin mutanen Jihar Kebbi
A tarihin siyasar 1999, inda aka dora a mulkin dimokudiyya, ma’ana siyasa a kasar nan tun lokacin da mulkin Jihar Kebbi ya fada a hannun jarumi, kuma garkuwa wanda a siyasar jihar ta Kebbi ba ta kammaluwa ba tare da jarumi kuma Garkuwan Gwandu, Alhaji Adamu Aliero irin ci gaban da ya kawo wa jiharsa […]
A tarihin siyasar 1999, inda aka dora a mulkin dimokudiyya, ma’ana siyasa a kasar nan tun lokacin da mulkin Jihar Kebbi ya fada a hannun jarumi, kuma garkuwa wanda a siyasar jihar ta Kebbi ba ta kammaluwa ba tare da jarumi kuma Garkuwan Gwandu, Alhaji Adamu Aliero irin ci gaban da ya kawo wa jiharsa ta haihuwa wajen nema ma matasa aiki da gina gidaje masu rahusa, samar da ruwan sha ga yankunan guda hudu, wadanda suka hada da Argungu da Gwandu da Yawuri da Zuru, wajen ganin al’ummomin sun samu ruwan sha mai inganci. Ya kuma gina ko gyaran hanyoyin ciki da wajen jihar zuwa manyan garuruwan nan hudu da kuma wadda ta hada kasar nan da makwabciyar jihar, wato Nijar, ta hada da kuma Argungu zuwa Sokwatto da illo zuwa malabin da Bena zuwa kantagora da dai sauran ayyuka raya kasa.
Bayan haka ya mayar da makaranta kimiya da fasaha ga gwamnatin tarayya, da gina jami’ar jiha a garin Aliero, da bai wa ‘yan asalin jihar tallafi wajen karo ilimi a manyan makarantun gaba da sakandare, a nan cikin gida da kuma wajen kasar nan; ya kara gina makarantun sakandare a fadin jiha na kwana da kuma na jeka ka dawo.
Tsohon gwamna ya raya bikin kamun kifi wanda ake gudanarwa duk bayan shekaru, domin samun kudin shiga ga jihar, wanda ake kira “Argungu International Fishing and Cultural Festibal” domin kara dankon zumunci tsakanin al’ummar kasar nan da kasashen waje.
Lallai rabuwa da gwani maye gurbinsa ke da wuya, kadan daga cikin ayyukan da tsohon gwamna, kuma tsohon ministan babban birnin tarayya Alhaji Adamu Aliero ya yi wa jiharsa ke nan, sabanin wannan gwamnati mai ci .