Adamu Garba: Mai gadin da ya zama malamin jami’a
Adamu Garba dan asalin Karamar Hukumar Sardauna a Jihar Taraba ne da aka dauke shi aiki a matsayin mai gadi a Jami’ar Tarayya da ke Wukari a jihar amma yanzu ya zama malami a jami’ar bayan ya yi karatun digiri. Aminiya ta tattauna da shi kan yadda haka ta faru: Mene ne takaitaccen tarihinka? […]
Adamu Garba dan asalin Karamar Hukumar Sardauna a Jihar Taraba ne da aka dauke shi aiki a matsayin mai gadi a Jami’ar Tarayya da ke Wukari a jihar amma yanzu ya zama malami a jami’ar bayan ya yi karatun digiri. Aminiya ta tattauna da shi kan yadda haka ta faru:
Mene ne takaitaccen tarihinka?
Sunana Adamu Dauda Garba, an haife ni a kauyen Tep da ke gundumar Nbamga a Karamar Hukumar Sardauna da ke nan Jihar Taraba a ranar 10 ga Oktoban 1985.Kafin a sanya ni a makarantar firamare na yi kiwon shanun mahaifina daga bisani aka sanya ni a firamare da ke garin Nbamga. Tsakanin kauyenmu zuwa Nbamga akwai nisa, amma nisan bai hana ni zuwa makaranta a kan lokaci ba. Na kammala firamare a 1998, sai na shiga sakandare da ke garin Gembu. A shekarar 2002 na kammala makarantar sakandare daga baya na shiga Kwalejin Ilimi da ke garin Jalingo.
A shekarar 2012 na kammala Kwalejin Ilimi da ke Jalingo na samu takardar shaidar NCE sai aka nemi masu sun aikin gadi a Jami’ar Tarayya da ke Wukari. Ban nuna girman kai ba, na nema aka dauke ne aiki.
Na yi kusan shekara biyar ina aikin gadi (security guard) sai aka samu sabon Shugaban Jami’a Furfesa Abubakar Kundiri. Shi ne ya bayar da umarnin cewa duk ma’aikacin jami’ar da bai da digiri kuma ya cika ka’idojin shiga jami’a ya yi karantun digiri to a ba shi damar yin karatu.
Wannan ce damar da na samu na karanta darasin sanin halayyar dan Adam wato Sociology inda na samu nasara a jarrabawar fita. Na fara karatun digiri a shekarar 2016 na kammala a bana, inda na kammala da mataki na biyu daraja ta daya wato Second Class Upper Dibision. Sai kuma ga wata dama inda jami’ar ta bai wa wadanda suka samu nasara damar canja sashin da suke aiki, aka mai da ni bangaren koyarwa wato lakcara inda a yanzu ina matsayin mataimakin lakcara. An dauke ni aiki ne a wannan wata na Disamba .
Ku nawa ne kuka samu irin wannan dama a jami’ar?
Muna da yawa wadanda muka yi karatun digiri kuma aka canja mana wajen aiki. Ban zan taba mantawa da wannan dama da Farfesa Abubakar Kundiri ya ba mu ba. Muna yi masa fatar alheri, Allah Ya taimake shi.
Mene burinka a nan gaba?
An ce ba a maraya sai rago da yardar Allah zan ci gaba da neman ilimi domin in zama cikakken malamin jami’a. A nan burina shi ne in zama mai babban digiri wato digirin digirgir (PhD).