Adamu Garba ya fasa neman takara bayan samun gudunmuwar N83.2m

Zan mayar wa da wadanda suka bayar da gudunmuwa kudadensu.

Adamu Garba ya fasa neman takara bayan samun gudunmuwar N83.2m

Adamu Garba

Daya daga cikin masu sha’awar neman takarar kujerar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Adamu Garba, ya jingine kudirinsa, bayan samun gudunmuwar Naira miliyan 83.2 domin sayen fom.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Talata a Abuja, Adamu Garba ya ce ya jingine aniyarsa ce saboda tsadar fom din neman takarar da jam’iyyar APC mai mulki a kasar ta tsawwalawa kudi.

A cewarsa, sanya Naira miliyan 100 a matsayin farashin fom din neman takarar da jam’iyyar APC ta yi  babu abin da zai haifar face mayar da siyasar Najeriya wajen cin kasuwa ba shugabanci na kwarai ba.

Ya ce ya yanke shawarar janyewa bayan tuntuba da neman shawarwarin kwamitin yakin neman zabensa, wanda kawo yanzu sun samu gudunmuwar Naira miliyan 83.2 daga wajen daidaikun masoya da magoya baya.

A kan haka ne Adamu Garba ya ce zai mayar wa da wadanda suka bayar da gudunmuwar kudadensu, sannan nan ba da jimawa ba zai sanar da shirinsa na gaba a harkar siyasa nan da kwanaki masu zuwa.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50