Adamu Lamido direban motar daukar jaridun Trust ya kwanta dama

A ranar asabar din da ta gabata ne Allah Ya yi wa Adamu Lamido direban motar Sifawa Line mai daukar jaridun kamfanin Media Trust rasuwa sakamakon hadarin da ya faru da shi a garin Takai ta Jihar Kano.Adamu wanda ake yi wa inkiya da Double Sigina, ya yi hadarin ne da misalin karfe 6:00 na […]

Adamu Lamido direban motar daukar jaridun Trust ya kwanta dama
Adamu Lamido direban motar daukar jaridun Trust ya kwanta dama

A ranar asabar din da ta gabata ne Allah Ya yi wa Adamu Lamido direban motar Sifawa Line mai daukar jaridun kamfanin Media Trust rasuwa sakamakon hadarin da ya faru da shi a garin Takai ta Jihar Kano.
Adamu wanda ake yi wa inkiya da Double Sigina, ya yi hadarin ne da misalin karfe 6:00 na safe bayan ya taso daga ofishin Media Trust na Kano dauke da jaridun Weekly Trust zuwa Gombe.
Wakilinmu ya je gidan mahaifin marigayin da ke unguwar Tudun Wada Gombe, inda mahaifinsa Lamido Madaki Hakimin Wuro Jabe, a karamar Hukumar Funakaye ya bayyana jimaminsa game da rasuwar dansa.
Malam Lamido Madaki, ya ce a ranar Asabar da misalin karfe 6:00 Adamu ya bugo masa waya ya gaishe shi ya ce masa yana kan hanyar zuwa Gombe daga Kano dauke da jaridun Trust idan ya shigo zai karaso gida ya gaishe su, “karshen maganata da shi ke nan. Bayan kamar minti 30, sai wani makwabcina ya bugo min waya ina garin Wuro Jabe inda nake Hakimci ya ce dana Adamu ya yi hadari Allah Ya yi masa rasuwa, ina jin haka sai na ce Innalillahi wa’ innailaihi raji’un,” inji Lamido Madaki.
Babban wan marigayin Ahmad Rufa’i ya ce yana da kanne fiye da 30 amma babu wanda ya fi shiga ransa kamar Adamu saboda mutum ne mai kwazon nema abin kansa.
Adamu ya rasu yana da shekara 31 kuma ya bar mace daya mai juna biu mai suna Lami da kuma ’ya’ya uku tuni aka yi jana’izarsa a can garin Takai kamar yadda Musulunci ya tanada bisa amincewar iyayensa.