ADC na neman Gawuna ya tsaya mata takarar Gwamnan Kano
Manyan jiga-jigan ADC na ci gaba da tattaunawa da makusantan Gawuna da nufin shawo kansa ya amince da tayin.
Nasiru Yusuf Gawuna
Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar ADC na ƙoƙarin jawo tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, domin ya tsaya mata takarar gwamna a Zaɓen 2027.
Jaridar Daily Nigeria ta ruwaito cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar na ci gaba da tattaunawa da makusantan Gawuna da nufin shawo kansa ya amince da tikitin takarar gwamna na ADC.
- HOTUNA: Sojoji sun ceto mata da yara 360 da Boko Haram ta sace a Borno
- Tsohon shugaban Gidan Rediyon Kano, Adamu Getso ya rasu
Majiyoyi sun bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, da tsohon jakada, Faruk Yabo, na daga cikin waɗanda ke ƙoƙarin shigar da Gawuna cikin jam’iyyar.
Rahoton ya kuma ce wannan na iya kasancewa daga cikin dalilan da suka sa har yanzu shugabancin ADC na ƙasa bai bayyana wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar gwamnan Kano tsakanin Malam Ibrahim Khalil da Ibrahim Little ba.
Sai dai har zuwa, babu wata sanarwa a hukumance daga ADC ko kuma Gawuna da ke tabbatar da wannan yunƙuri.