ADC za ta yi zanga-zanga kan neman Amupitan ya yi murabus daga shugabancin INEC

Jam’iyyar ta buƙaci Amupitan ya yi murabus nan take daga muƙaminsa.

ADC za ta yi zanga-zanga kan neman Amupitan ya yi murabus daga shugabancin INEC

Jam’iyyar ADC, ta buƙaci Farfesa Joash Amupitan, ya sauka daga muƙaminsa na shugabancin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Jam’iyyar ta yi wannan kira ne bayan wasu sabbin zarge-zarge da suka bayyana a kansa.

An ruwaito cewar wasu tsofaffin rubuce-rubucen da Amupitan ya yi a kafafen sada zumunta, sun nuna yana goyon bayan jam’iyyar APC.

Hukumar INEC ta bakin mai magana da yawunta ta buƙaci jama’a su yi watsi da zarge-zargen inda ta danganta su a matsayin ƙarya, tare da jaddada ƙudirinta na gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.

Sai dai fitaccen malamin jami’ar nan ɗan Najeriya da ke zaune a Amurka, Farooq Kperogi, ya ce wasu tsofaffin rubuce-rubuce da ake alaƙanta Amupitan sun yana goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce hakan na iya rage amincewar jama’a dangane da sahihancin INEC.

Batun ya janyo muhawara mai zafi a tsakanin ’yan Najeriya, musamman a kafafen sada zumunta, inda ra’ayoyin mutane suka bambanta kan gaskiyar waɗannan rubuce-rubuce.

Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce lamarin yana da matuƙar muhimmanci kuma zai iya shafar amincewar jama’a da tsarin zaɓe.

Ya buƙaci Amupitan ya yi murabus nan take.

Jam’iyyar ta kuma ce za ta ci gaba da zanga-zanga da ɗaukar wasu matakai har sai shugaban INEC ya sauka daga muƙaminsa.