Addini da kabilanci a siyasa

Mutanenmu da yawa na da karancin sanin sha’anin siyasa, shi isa za ka ga wani sashi na mabambanta ra’ayi a siyasance na jin haushi ko cin zarafi ko shiga mutuncin mutum, saboda bambancin ra’ayi na Siyasa, wanda hakan kuskure ne kuma ba tarbiyya ba ce ta addini.A ka’ida bai kamata sabani ko ra’ayin siyasa ya […]

Addini da kabilanci a siyasa
Addini da kabilanci a siyasa

Mutanenmu da yawa na da karancin sanin sha’anin siyasa, shi isa za ka ga wani sashi na mabambanta ra’ayi a siyasance na jin haushi ko cin zarafi ko shiga mutuncin mutum, saboda bambancin ra’ayi na Siyasa, wanda hakan kuskure ne kuma ba tarbiyya ba ce ta addini.
A ka’ida bai kamata sabani ko ra’ayin siyasa ya sabbaba kawo shiga mu’amalar zamantakewa ba. Kuma duk dimokuradiyyar da babu kalubale a cikinta, to wadanda ake shugabanta ba za su moreta ba sam-sam.
Wannan dalilin ne yasa aka yi jam’iyyun da dama, kuma aka bai wa kowanne mai irin nau’in addini da marasa addini damar shiga kowace, don a bawa ‘yan kasa su samu damar zabar ra’ayinsu bisa ra’ayin da ya yi musu a karan kansu, ta yadda za a dama da kowa.
Kuma ta hanyar hadin kaine da mantawa da bambancin yare da addini ne kawai za mu isa tudun mun tsira, a irin wannan kasar da Allah ya kaddara rayuwa a cakude tsakanin Musulmi da Kirista da marasa addinai. Allah ya datar da mu.
Idan ka kalli Najeriya a matsayin kasa daya, al’umma daya da rabe-raben addinai mabambanta za ka iya zbar Musulmi ko Kirista, idan kuma kana da ra’ayin addini ko kabilanci to za ka iya zaben Musulmi ko kabila.
Shi kuwa Kirista zai iya zabar Kirista ko kabila. Amma kada ka manta ba a cin zaben Najeriya da sashi daya kacal. Saboda kowanne sashi na neman taimakon kuri’un sashe.
Abin da yawanmu ba sa  ganewa ko fahimtarmu har kullun shi ne; idan ka fahimce ni sosai za ka gane alkiblata.  Ina me kara tabbatar maka na gamsu da tsari da tarbiyya irin ta Minista  Sardauna da ta kai ta fuskar addini da tsarin gudanarwar rayuwasu. Kuma alakarka da mai sabanin ra’ayinka ko fahimtarka, ba shi ke nuna taimakon addininsa ba, saboda idan ba mu jahilci tarihi ba za muga inda Annabi(S.A.W.) ya gudanar da rayuwarsa da wadanda ba su yi imani da shi ba, kuma zama da su bai cutar da Addinin Islama ba, sai ma daukaka da tagomashi da ya kara samu.
Ba wata siyasa a kasar nan muddin kana son samun nasara da za ka alakantata da wani addini ko yanki ko kabila da za ka sa ran tayi tasiri ko cin nasara. Wato wannan maganar  ko ra’ayi ita ta hana tsohuwar Jam’iyyar Adawa ta APP (ANPP) da CAN da CPC da sauransu cin galaba
da nasara a wurin Jam’iyyar PDP, wadda har yanzu da suka hade suka cure wuri guda ba su shirya karbar Najeriya sam daga wurin PDP ba. Sakamakon tasirin kabilanci da bangaranci da ya dabaibaye jam’iyyar, musanman daga yankinmu na Arewa.
Idan mai biye da ni ya saurari taron da jam’iyyar ta gudanar na zaben shugabannita, a ranakun Juma’a da Asabar 23-14/06/2014 a Abuja, za ka ji, inda jagororin ke bayyana wa jama’ar  kasa da magoya bayansu cewa jam’iyyarsu ba ta Musulmai ba ce, ba ta Kirista ba ce;
ta kowa da kowace. Ma’ana ta kowanne nau’in mai addini ne ko mara addini. Har yanzu ba siyasa ce ta Addini ba, don ba ka iya rabewa tsakanin addini da rayuwa, tun da tare suke tafiya da juna a matakin rayuwa. Kuma alaka tsakanin Musulmi da mabiyin wani addini, wata hadaka ce da Allah ya gina rayuwa a kanta tun farko halittar duniya, kamar  yadda Allah ya halicci dan Adam a gefe guda, kuma ga Iblis (Shaidan). hHaka kaddarar rayuwa ta tsaru kuma ta kasance abokina.
Wato an samu bullar kofar rashin hadin kai  ke nan da zarar an bayyanar da bangaranci ko kabilanci, shi yasa nake fada wa mai karatu APC ba ta shirya ba, in dai akwai masu kudurcewa a ransu jam’iyyar ta addininsu ce.
Yanzu kana nufi dan Kudu, wanda ba Musulmi ba, ya zabi Musulmi haka Allah ya kaddara kana da wannan ra’ayin kuma kana bayyanar da shi suna jinka???
Allah ya yi amfani da rayuwarmu da lafiyarmu wajen zabo shugabanni nagari masu  kishin kasata Nijeriya, ba tare da nuna bambanci da kabilanci ko zaluntar wani yanki ba a kowacce jam’iyya suke.
Za a iya tuntubar Muhammad ta i-mail dinsa: [email protected]

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya