Addinin Kirista bai yarda da daukar doka a hannu ba – Injiniya Kazai

Injiniya Daniel Kazai shi ne Shugaban Matasa Kiristoci na Arewa, a tattaunawansa da wakilinmu a Lafiya ya bayyana hanyoyin magance matsalolin da kasar nan ke fuskanta da wasu batuttuwa da suka shafi zaman lafiya a tsakanin Kiristoci da Musulmi musamman matasa:Me za ka ce game da rashin tsaro da ya zama ruwan dare a kasar […]

Addinin Kirista bai yarda da daukar doka a hannu ba – Injiniya Kazai
Addinin Kirista bai yarda da daukar doka a hannu ba – Injiniya Kazai

Injiniya Daniel Kazai shi ne Shugaban Matasa Kiristoci na Arewa, a tattaunawansa da wakilinmu a Lafiya ya bayyana hanyoyin magance matsalolin da kasar nan ke fuskanta da wasu batuttuwa da suka shafi zaman lafiya a tsakanin Kiristoci da Musulmi musamman matasa:
Me za ka ce game da rashin tsaro da ya zama ruwan dare a kasar nan?
Halin da muka same kanmu yau a Najeriya hali ne na ban takaici da kaito. Idan ka wayigari kullum za ka ji an kashe mutane kaza an kashe mutane kaza ko a ce mutane kaza sun bace. Labarar irin na tada hankali za ka rika ji kullum. Ba ranar da za a wayigari ba a ji an kashe mutane ko an sace mutane ba. Wasu suna tunanin cewa matsalar kasar nan Boko Haram ne kawai bayan a Najeriya yau ana da kamfanin yin yara. Ana haifar yara ana sayar da su kuma wadannan mutane an san su a kasar nan, sun kama wuri sun tara ’yan mata da maza ana hada su suna haifar jarirai ana sayar da su don son kudi. A kasar nan yau ana sace mutum a tsare shi sai an biya diyya. Ga barayi a duk hanyoyinmu duk da jami’an tsaro da ke hanyoyin. A gwamnati kuma ana satar fitar hankali inda, biliyoyin Naira suke bacewa kullum daga asusun gwamnati. Sai ka rasa me mutum zai yi da irin wadannan makudan kudi. Wani abin takaici kuma shi ne a da idan mutum ya sa tufafin da ya yi kama da na ’yan sanda ko soja za a kama shi a hukunta shi. Amma yanzu ana sa tufafin wadannan jami’an tsaro ana kashe mutane ba abin da ke faruwa. Saboda haka akwai matsaloli da dama da ke damunmu a kasar nan, ba Boko Haram ne kawai ba.
To, me kake gani ke jawo wadannan matsaloli?
Kodayake a nawa ra’ayi zan iya ce maka cikar Annabta ce. Domin a Littafi Mai tsarki Allah Ya ce a karshen zamani za a shiga mawuyacin hali, mutane za su zama masu son kansu, masu son kudi, ’ya’ya za su yi gaba da iyayensu. kasashe za su yi gaba da kasashe da dai sauransu. Mutane yau sun zama masu son kudi sosai. Duk abubuwan da na bayyana a baya duk a kan kudi ne ake aikatawa. Idan mutum ya bdde kamfanin sarrafa yara jarirai ba kudi yake nema ba? Haka wadanda ke garkuwa da mutane duk kudi suke nema. Haka abin yake a gwamnati, ba ka ji kwanakin baya mutum ne ana tuhumansa da laifin sace kudi masu yawa sai aka ce a yi belinsa kan Naira dubu 70 kawai. Wato kamar a ce ka je ka saci giwa ne sai a zo a ce ka kawo fara don a sake ka. Son kudi yau ya shiga har bangaren addini a kasar nan don an daina wa’azin gaskiya yanzu saboda son kudi. Ana kuma karya wanda ke da takardar mota ba za a bar shi ya wuce a hanya ba sai mai kudi. Mutum ne wasu shugabannin coci sun san shi barawo ne maimakon a zaunar da shi a mai wa’azi ya tuba. Amma sai a masa addu’a Allah Ya kare shi kada a kama shi. Masu yin haka suna nan da yawa mun san su. Wani abin takaici kuma shi ne yadda shugabanninmu da muke ganin za su kare mana mutunci amma idan ka ji irin kalaman da suke yi wa junansu saboda kudi sai ka yi kuka. Maimakon su yi abin da zai taimaki jama’a sai su rika yin wadanda zuciyarsu ke so kawai a koyaushe. Ga sarakunan gargajiyarmu yau sun shiga siyasa su ma. Shi ya sa nayi farin ciki sosai da nake karanta a wata jarida inda, Sarkin Musulmi Mai martaba Sa’ad Abubakar ke yin kira ga sarakuna su kaurace wa siyasa. Da su da shugabannin addinai duk ya kamata su yi nesa da harkokin siyasa. Kowa ya tsaya ga aikinsa, ka ga shawara ce mai kyau. Saboda haka akwai abubuwa da dama da ke jawo wadannan tashin-tashina amma muhimmansu su ne kamar yadda na bayyana maka son kai da son kudi wato rashin wadatar zucci.
A matsayinku na shugabannin addinai musamman na matasa da ake amfani da su wajen ta da fitina. Me kuke yi don jawo hankalinsu?  
Abu na farko da muke yi kullum shi ne addu’a, don idan ka yi addu’a Allah zai ba ka basirar da za ka iya shawo kan kowane lamari. Kuma kamar yadda kamannin mutane ke daban-daban haka hanyoyin sadar musu da sakon zaman lafiya yake. Sau da yawa mukan kira taro inda muke fahimtar da su a kan hadarin da ke tattare da fitina. Haka muna kokarin wayar musu da kai a kan su nemi abin kansu kamar karatu da sana’o’i don taimaka wa rayuwarsu maimakon su bari wasu na amfani da su wajen tada fitina da a karshe za su yi da-na-sani. Kodayake wasu matasa da ake amfani da su wajen tada fitinun nan ina tabbatar maka cewa ba da son ransu ba ne. Idan ka lura shugabanninmu yau kyauta suka yi makarantarsu ba su biya ko kwabo ba. Abincinsu da sutura da takardunsu komai dai kyauta aka samar musu. Amma ba haka lamarin yake ya au ba. Kuma da zarar ka kammala karatunka za ka samu aikin yi. Amma yau matasa wasu cikinsu ba su da aikin yi duk da cewa sun kammala karatunsu da dadewa. To, yaya za a samu zaman lafiya a kasar nan? Saboda haka kamar yadda muke kokari wajen tabbatar matasan nan sun daina tada fitinu ya kamata gwamnototi a dukkan matakai su tashi su kirkiro shirye-shiryen da za su samar wa matasa da aikin yi don rage zaman banza.
Wasu na cewa rigirgimu musamman a nan Arewa suna da alaka da addini, mene negaskiyar lamarin?
A gaskiya batun tashin hankali da ke haifar da kashe-kashe da garkuwa da jama’a da fashi da makami da fashewar bam da sauransu da suka addabi kasar nan, wadanda ke aikatawa da aka kama a halin yanzu Kiristoci ne kawai ko Musulmi ne kawai. Tambayar da ya kamata masu cewa rigirgimun suna da alaka da addini su tambayi kansu ke nan. Wadannan miyagun mutane suna kashe Musulmi da Kiristoci baki daya, abin ke faruwa a Arewa yau wani bala’i ne da ya shigo tsakaninmu baki daya da muke rokon Allah Ya kawo mana karshensa. Kiristoci na mutuwa Musulmi na mutuwa saboda haka ba zaka tashi ka ce wannan abu na da alaka da addini ko kusa.  
Sau da yawa idan aka kashe Kirista ko aka kone coci a nan Arewa za ka ga wasu matasa Kiristoci suna zanga-zanga, suna barazanar kone masallatai da sauransu. Me kuke yi a matsayinku na shugabannin matasan a irin wannan lokaci?
A gaskiya na ji dadin wannan tambaya, kwarai da gaske hakan na faruwa. Kuma mu shugabannin matasa ba ma zama da mun ji haka. Domin babban aikinmu shi ne tabbatar da zaman lafiya a tsakanin matasa Kiristoci da wadanda ba Kiristoci ba a kasar nan. Nakan tafi da kaina in gargade su bayan na kwantar musu da hankali ina gaya musu cewa wadannan mutane da suka aikata laifin nan na tabbata ba Musulmin kwarai ba ne. Kuma ina jawo hankalinsu cewa su guji daukar fansa domin ransu ya baci. Don ba ka san abin da ka iya biyo baya ba. Mukan gargade su cewa maimakon daukar doka a hannunsu su rika kai kara ga hukumomin da suka da ce. Kuma ina so yin amfani da wannan damar in yi kira ga ’yan uwana matasa Kiristocin Arewa da kasa baki daya su guje wa daukar doka a hannunsu a duk lokacin da irin wannan lamari ya auku kodayake ba ma fata ya faru.