Addu’a

Muna yi wa Ubangiji Godiya domin yawan alheri da kaunarSa zuwa gare mu a koyaushe.  Barkanmu da sake haduwa cikin wannan sabon wata na Maris. Alherin Ubangiji ne kadai ya sa muka kasance cikin rayayyu a yau, daukaka ga sunanSa. A wannan karo za mu yi nazari ne a kan addu’a. A wannan makon kuwa […]

Addu’a

Muna yi wa Ubangiji Godiya domin yawan alheri da kaunarSa zuwa gare mu a koyaushe. 

Barkanmu da sake haduwa cikin wannan sabon wata na Maris. Alherin Ubangiji ne kadai ya sa muka kasance cikin rayayyu a yau, daukaka ga sunanSa.

A wannan karo za mu yi nazari ne a kan addu’a. A wannan makon kuwa za farko za mu duba kima daga cikin addu’o’in da ke cikin Littafi Mai tsarki da Yesu Almasihu ya koya wa almajiransa, sannan wadanda Yunusa da Sarki Dauda da Hannatu da Yabez  suka yi, sannan za mu bi su daya bayan daya don mu fahimce su. 

 

Addu’ar Ubangiji

Matiyu 6:9-13

Saboda haka sai ku yi addu’a kamar haka, ‘Ya Ubanmu, wanda Yake cikin sama, A kiyaye sunanKa da tsarki. MulkinKa ya zo, A aikata nufinKa a duniya kamar yadda ake yi a sama. Ka ba mu abincinmu na yau. Ka gafarta mana laifuffkanmu, Kamar yadda mu ma muke gafarta wa wadanda suke yi mana laifi. Kada Ka kai mu wurin jaraba, Amma Ka cece mu daga mugun.’

 

Addu’ar godiya ga Ubangiji

Yunusa 2:2-9

Sai Yunusa ya yi addu’a ga Ubangiji Allah a cikin cikin kifin, ya ce, “A cikin wahalata na yi kira gare Ka, ya Ubangiji, Ka kuwa amsa mini. Daga can cikin Lahira na yi kira, Ka kuwa ji muryata. Ka jefa ni cikin zurfi, can cikin tsakiyar teku, inda igiyoyin ruwa suka kewaye ni, Kumfa da rakuman ruwanKa suka bi ta kaina. Na ce, an kore ni daga wurinKa, Duk da haka zan sake ganin Haikalinka mai tsarki. Ruwa ya sha kaina, Tekun ta rufe ni dungum. Tsire-tsiren teku suka nade kaina. Na tafi can kasa karkashin tussan duwatsu. kasar da kofarta ke rufe har abada, Amma Ka fitar da ni daga cikin ramin, ya Ubangiji Allahna. Sa’ad da na ji raina yana rabuwa da ni, Sai na tuna da Kai, ya Ubangiji. Addu’ata kuwa ta kai gare Ka a Haikalinka tsattsarka. Su wadanda ke yin sujada ga gumaka marasa amfani sun daina yi maKa biyayya. Amma ni zan raira yabbai gare Ka, Zan mika maka sadaka, Zan cika wa’adin da na yi. Ceto daga wurin Ubangiji yake.” Ubangiji kuwa Ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunusa a gabar teku.

 

Addu’ar dogara ga Ubangiji 

Zabura 3

Ina da makiya da yawa, ya Ubangiji, Da yawa kuma sun juya, suna gaba da ni! Suna magana a kaina, suna cewa, “Allah ba zai taimake shi ba!” Amma Kai, ya Ubangiji, kullum Kana kiyaye ni daga hadari, Kana ba ni nasara, Kana kuma maido mini da karfin halina. Na yi kira wurin Ubangiji domin taimako, Ya kuwa amsa mini daga tsarkakken dutsenSa.

Na kwanta na yi barci, Na kuwa tashi lafiya lau, Gama Ubangiji Yana kiyaye ni. Ba na jin tsoron dubban abokan gaba wadanda suka kewaye ni ta kowane gefe. Ka zo, ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka yi nasara a kan dukan abokan gabana, Ka hallakar da dukan mugaye. Ceto yana zuwa daga wurin Ubangiji, Bari Ya sa wa jama’arsa albarka!

 

Addu’ar yabo ga Ubangiji

1 Samaila 2:1-10

Hannatu kuwa ta yi addu’a ta ce, “Ubangiji Ya cika zuciyata da murna. Ina farin cikin da abin da Ya yi. Ina yi wa makiyana dariya, Ina matukar murna domin Allah Ya taimake ni. “Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji, Babu wani mai kama da Shi, Ba mai kiyaye mu kamar Allahnmu. Kada ku kara yin magana ta girman kai, Ku daina maganganunku na fariya, Gama Ubangiji Allah Shi ne Masani, Yana kuma auna dukkan aikin da mutum ya yi. An kakkarya bakunan karfafan sojoji, Amma rarrauna ya zama mai karfi. kosassun mutane suna kwadago saboda abinci, Masu fama da yunwa kuwa sun daina jin yunwa. Bakarariya ta haifi ’ya’ya bakwai, Wadda ta haifi ’ya’ya da yawa kuwa ta rasa su duka. Ubangiji ne Yake kashewa, Ya kuma rayar, Yana kai mutane kabari, Ya kuma ta da su. Yakan sa wadansu mutane su zama matalauta, Wadansu kuwa attajirai. Yakan kaskantar da wadansu, Ya kuma daukaka wadansu. Yakan ta da matalauci daga cikin kura, Yakan daga mai bukata daga zaman bakin ciki. Ya sa su zama abokan ’ya’yan sarki, Ya dora su a wurare masu makami. Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne, A kansu ya kafa duniya. Zai kiyaye rayukan amintattun mutanensa, Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu, Ba karfin mutum yake sa ya yi nasara ba. Za a hallakar da makiyan Ubangiji, Zai yi musu tsawa daga sama. Ubangiji zai hukunta dukan duniya, Zai ba sarkinsa iko, Zai sa zababben sarkinsa ya zama mai nasara.”

 

Addu’ar roko daga wurin Ubangiji

1 Tarihi 4:9-19

Yabez ya fi sauran ’yan uwansa kwarjini saboda haka mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, wato da wahala ta haife shi. Yabez ya roki Allah na Isra’ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, Ka fadada kan iyakata, hannunKa kuma ya kasance tare da ni, Ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa Ya biya masa bukatarsa.

Da yardar Ubangiji, mako mai zuwa zamu fara da addu’ar Ubangiji wanda Yesu Almasihu ya koya wa almajiransa.

Shalom.