Addu’a (3)
Addu’ar godiya ga Ubangiji Godiya ta tabbata ga Ubangiji domin kaunarsa zuwa gare mu. Barkanmu kuma da sake haduwa domin mu ci gaba da nazari a kan yin addu’a. Makon jiya mun yi nazari ne a kan addu’ar Ubangiji, a makon nan kuwa za mu yi bincike ne a kan addu’ar godiya ga Ubangijimu. Cikin […]
Addu’ar godiya ga Ubangiji
Godiya ta tabbata ga Ubangiji domin kaunarsa zuwa gare mu. Barkanmu kuma da sake haduwa domin mu ci gaba da nazari a kan yin addu’a.
Makon jiya mun yi nazari ne a kan addu’ar Ubangiji, a makon nan kuwa za mu yi bincike ne a kan addu’ar godiya ga Ubangijimu.
Cikin komai a rayuwan nan ya kamata mu zama masu godiya ga Ubangiji domin girmanSa da kuma kaunarSa zuwa gare mu, hatta cikin kowane hali muka tarar da kanmu, “Ku yi godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu.” (1 Tasalonikawa 5:18).
Ubangiji Mai kauna ne, Mai rahama, Mai jinkai kuma a koyaushe cikin kowane hali. Zabura 103:1-5, 136:1-5, tana cewa, “Ka yabi Ubangiji, ya raina! Ka yabi sunanSa Mai tsarki! Ka yabi Ubangiji, ya raina, Kada ka manta da yawan alherinSa. Ya gafarta dukan zunubaina, Ya kuma warkar da dukan cututtukana. Ya cece ni daga kabari, Ya sa mini albarka da kauna da jinkai. Ya cika raina da kyawawan abubuwa, don in zauna garau, kakkarfa kamar gaggafa. Ku gode wa Ubangiji domin Shi mai alheri ne, Gama kaunarSa madauwamiya ce. Ku gode wa Allahn da Ya fi dukan alloli girma, Gama kaunarSa madauwamiya ce. Ku gode wa Ubangijin dukan iyayengiji, gama kaunarSa madauwamiya ce. Shi kadai ne yake aikata mu’ujizai masu girma, Gama kaunarSa madauwamiya ce. Ta wurin hikimarSa Ya halicci sammai, gama kaunarSa madauwamiya ce.”
Bari mu ga rayuwar wadansu a cikin Littafi Mai tsarki da za mu yi koyi da halin da suka nuna ta wurin shaida godiyarsu ga Ubangiji.
Luka 17:11-19, Wata rana [Yesu] yana tafiya Urushalima, sai ya bi iyakar kasar Samariya da Galili. Yana shiga wani kauye ke nan, sai wadansu kutare maza guda goma suka tarye shi, suna tsaye daga nesa. Sai suka daga murya suka ce, “Ya Maigida Yesu, ka ji tausayinmu!” Da ya gan su, ya ce musu, “Ku je wurin firistoci su gan ku.” Suna tafiya ke nan, sai suka tsarkaka. dayansu kuma da ganin an warkar da shi, ya komo, yana ta daukaka Allah da murya mai karfi, ya fadi a gaban Yesu, yana gode masa. Shi kuwa Basamariye ne. Yesu ya amsa ya ce, “Ba goma ne aka tsarkake ba? Ina taran? Ashe, ba wanda aka samu ya komo ya daukaka Allah, sai bakon nan kadai?” Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka. Ban-gaskiyarka ta warkar da kai.”
Abin koyi a nan shi ne, kada mu dauki alherin Ubangiji a banza, kada kuma yawan farin ciki ya samu mu manta da mika godiyarmu ga Ubangiji. Don za ka ga wadansu idan abin farin ciki ya same su, sukan manta nuna wa Ubangiji godiya da farko, sai ka ga sun hada bukukuwa, a yi ta hayaniya, ana ciye-ciye da shaye-shaye a bugu, har ma ta kai wadansu ga rasa rayukansu, sai mu yi lura da wannan.
Muna dai sane da labarin Annabi Yunusa cikin Littafi Mai tsarki cikin Littafin Yunusa 1-4, wanda Ubangiji Allah Ya aike shi zuwa kasar Nineba don fadakar da su domin yawan zunubansu, amma maimakon Yunusa ya tafi, sai ya gudu daga wurin Ubangiji zuwa Tarshish. Ya tafi Yafa, nan ya samu jirgin ruwa yana gab da tashi zuwa Tarshish, ya kuwa biya kudinsa, ya shiga tare da masu jirgin zuwa can don ya tsere wa Ubangiji, amma Ubangiji Ya aika da iska mai karfi a tekun, hadirin ya tsananta kwarai har jirgin yana bakin farfashewa… Ubangiji kuwa Ya umarci wani babban kifi ya hadiye Yunusa. Yunusa kuwa ya yi wuni uku da dare uku a cikin cikin kifin. A cikin cikin kifin kuwa Yunusa ya yi addu’a ga Ubangiji Allah.
A sura ta 2:2-9, “Sai Yunusa ya yi addu’a ga Ubangiji Allah a cikin cikin kifin, ya ce, “A cikin wahalata na yi kira gare Ka, ya Ubangiji, Ka kuwa amsa mini. Daga can cikin Lahira na yi kira, Ka kuwa ji muryata.
Ka jefa ni cikin zurfi, Can cikin tsakiyar teku, Inda igiyoyin ruwa suka kewaye ni, Kumfa da rakuman ruwanKa suka bi ta kaina. Na ce, an kore ni daga wurinka, Duk da haka zan sake ganin Haikalinka mai tsarki. Ruwa ya sha kaina, Tekun ta rufe ni dungum. Tsire-tsiren teku suka nade kaina. Na tafi can kasa karkashin tussan duwatsu. kasar da kofarta ke rufe har abada, Amma Ka fitar da ni daga cikin ramin, ya Ubangiji Allahna. Sa’ad da na ji raina yana rabuwa da ni, Sai na tuna da Kai, ya Ubangiji. Addu’ata kuwa ta kai gare Ka a Haikalinka tsattsarka. Su wadanda ke yin sujada ga gumaka marasa amfani sun daina yi maKa biyayya. Amma ni zan rera yabbai gare ka, Zan mika maka sadaka, Zan cika wa’adin da na yi. Ceto daga wurin Ubangiji yake.”
Ubangiji kuwa ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunusa a gabar teku.
Annabi Yunusa ya saba wa Ubangiji ta wurin rashin biyayya ga zuwa inda Ubangiji Ya aike shi, amma daga baya ya tuba ya kuma mika addu’ar godiya ga Ubangiji.
Za mu ci gaba mako mai zuwa da yardar Ubangiji.
Shalom.