Addu’a (4)

Addu’ar dogara ga Ubangiji:  ‘Ka mika kanka ga Ubangiji, Ka dogara gare Shi, zai kuwa taimake ka.’ (Zabura 37:5) Barkanmu da sake haduwa a wannan mako, Godiya ta tabbata ga Ubangiji Sarkin sarakuna domin ba mu wannan zarafi na kasancewa cikin rayyayu.  A wannan makon za mu yi nazari ne a kan addu’ar dogara ga […]

Addu’a (4)

Addu’ar dogara ga Ubangiji: 

‘Ka mika kanka ga Ubangiji, Ka dogara gare Shi, zai kuwa taimake ka.’ (Zabura 37:5)

Barkanmu da sake haduwa a wannan mako, Godiya ta tabbata ga Ubangiji Sarkin sarakuna domin ba mu wannan zarafi na kasancewa cikin rayyayu. 

A wannan makon za mu yi nazari ne a kan addu’ar dogara ga Ubangiji. 

Rayuwa tana cike da shakka, fargaba, tsoron gobe da na magabta. Mukan yi tunanin abin da zai faru gobe watakilla don yanayin da mutum ya tarar da kansa a ciki, ko abubuwan da suke faruwa kewaye da mu, ko kuma lokacin da magabta suka afko maka, musamman a cikin zamaninmu na yanzu. Abin farin ciki shi ne, Ubangiji Yana nan tare da mu a cikin kowane irin yanayi, Yana so mu zo gabanSa cikin addu’a mu mika maSa bukatunmu a gabanSa. Gama Littafi Mai tsarki yana cewa:

“Ka gabatar da wahalarka ga Ubangiji, Zai kuwa taimake ka, Ba zai bari a ci nasara a kan mutumin kirki ba, faufau. (Zabura 55:22).

“Ku zo gare Ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, Ni kuwa zan hutashe ku.” (Matiyu 11:28), “Kada ku damu da komai, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu’a da roko, tare da gode wa Allah. Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.” (Filibiyawa 4:6-7).

Kira ke nan da Ubangiji Ya yi ga duk wanda yana dauke da nauyin kaya, wato damuwa, tsoro, shakka, fargaba, da duk matsalolin rayuwa, Ubangiji Allah Yana cewa ka dogara gare Shi, ka mika maSa dukan bukatunka, Shi kuwa zai ji ka Ya kuma biya maka bukata. Bari mu samu karfafawa daga Sarki Dauda, ya dogara ga Ubangiji a lokacin da yake cikin wahala yana kuma fuskantar magabta. 

 (Zabura 3, 31:1-7, 46:1-3).

“Ina da makiya da yawa, ya Ubangiji! Da yawa kuma sun juya, suna gaba da ni! Suna magana a kaina, suna cewa, “Allah ba zai taimake shi ba!” Amma Kai, ya Ubangiji, kullum Kana kiyaye ni daga hadari, Kana ba ni nasara, Kana kuma mai do mini da karfin halina. Na yi kira wurin Ubangiji domin taimako, Ya kuwa amsa mini daga tsattsarkan dutsenSa.”

“Na kwanta na yi barci, Na kuwa tashi lafiya lau, Gama Ubangiji Yana kiyaye ni. Ba na jin tsoron dubban abokan gaba Wadanda suka kewaye ni ta kowane gefe. Ka zo, ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka yi nasara a kan dukan abokan gabana, Ka hallakar da dukan mugaye. Ceto yana zuwa daga wurin Ubangiji, bari Ya sa wa jama’arSa albarka!”

 “Na zo gare ka, ya Ubangiji, domin ka kiyaye ni. Kada ka bari a yi nasara da ni. Kai Allah Mai adalci ne, Ka cece ni, ina rokonKa! Ka ji ni! Ka cece ni yanzu! Ka zama mafakata, don Ka kiyaye ni, Ka zama mai kare ni, don Ka cece ni. Kai ne mafakata da kariyata, Ka bi da ni yadda Ka alkawarta. Ka kiyaye ni daga tarkon da aka kafa domina, Kai ne inuwata. Ina ba da kaina gare Ka domin Ka kiyaye ni. Za Ka fanshe ni, ya Ubangiji, Kai Allah Mai aminci ne. Kana kin wadanda suke yi wa gumaka sujada, Amma ni na dogara gare Ka.

Zan yi murna da farin ciki, Saboda madauwamiyar kaunarKa. Ka ga wahalata, Ka kuwa san damuwata. 

 “Allah ne Mafakarmu da karfinmu, Kullum a shirye Yake Ya yi taimako a lokacin wahala. Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, Ko da duniya za ta girgiza, Duwatsu kuma su fada cikin zurfafan teku, Ko da a ce tekuna za su yi ruri su tumbatsa, Tuddai kuma su girgiza saboda tangadin tekun.

 Bari dogararmu ta zamana bisa Ubangiji kadai, mu zama masu ba da gaskiya gare Shi kadai, gama idan muka dogara ga  mutum ko dukiyarmu domin biyan bukata da kariya, za mu yi asara.   

“Mutanen da suke dogara ga dukiyarsu, Wadanda suke fariya saboda yawan wadatarsu? Har abada mutum ba zai iya fansar wani ba, Ba kuwa zai iya biyan kudin ransa ga Allah ba. Gama kudin biyan ran mutum ba shi da iyaka. Abin da zai iya biya, sam ba zai isa ba, Ba kuwa zai rayar da shi, Ko ya hana shi mutuwa har abada ba. Yakan sa masu hikima su ma su mutu, Haka nan ma wawaye da mutanen banza, Za su mutu su bar dukiyarsu ga zuriyarsu. Kaburburansu za su zama gidajensu har abada, Can za su kasance kullum, Ko da yake a da suna da kasa ta kansu. Girman mutum ba zai hana shi mutuwa ba, Zai mutu kamar dabba. Dubi abin da zai faru ga wadanda suke dogara ga kansu, Da irin kaddarar wadanda dukiya ta ishe su. Za a kaddara su ga mutuwa kamar tumaki, Mutuwa ce za ta yi kiwonsu. Da safe adalai za su ci nasara a kansu, Sa’ad da gawarwakinsu suke rubewa a kasar matattu, Nesa da gidajensu. Amma Allah zai fanshe ni, Zai dauke ni daga ikon mutuwa.” (Zabura 49:6-15). 

Domin haka, sai mu mika kanmu ga Ubangiji kadai don biyan bukatunmu.” 

Ubangiji Ya taimake mu, amin.