Addu’a (7)

Yin karya Muna yi wa Ubangiji Allah godiya domin kaunarSa zuwa gare mu. BarkaRmu da sake haduwa a wannan makon inda za mu yi nazari a kan yin karya. Yin karya abu ne da mutane da dama a yau ba su dauke shi laifi ba a gaban Ubangiji da kuma gaban mutum. Babu shakka babu […]

Addu’a (7)

Yin karya

Muna yi wa Ubangiji Allah godiya domin kaunarSa zuwa gare mu. BarkaRmu da sake haduwa a wannan makon inda za mu yi nazari a kan yin karya.

Yin karya abu ne da mutane da dama a yau ba su dauke shi laifi ba a gaban Ubangiji da kuma gaban mutum. Babu shakka babu mutumin da zai so wani ya gaya masa abin da ba gaskiya ba, ba kuwa wani da zai so ya yi alaka da mayaudari, balle kuma Ubangiji Mahaliccinka! “Ubangiji Yana kin makaryata, amma Yana murna da masu fada da cikawa.” Karin Magana 12:22. Yaya za ka ji idan ka yaudari mahaifinka ko mahaifiyarka? Yaya kuma za ka ji a zamanka/ki na uba ko uwa idan ’ya’yan cikinka suka yaudare ka?  Yin karya abu ne da ya kamata mu yi tunani a kai kwarai da gaske mu kuma dauki mataki a kai. A wasu lokuta mukan iya samun kanmu a wani hali da za mu ga kamar yin karya ne kadai mafita, amma mun taba sanin cewa idan muka nemi nufin Ubangiji cikin komai zai ji mu Ya kuma taimake mu. Masu iya magana sukan ce ‘gaskiya dokin karfe,’ mai yi ko fadin gaskiya a koyaushe mai nasara ne kai-tsaye. Makaryaci kuma ba zai taba samun salama da kwanciyar hankali ba ko kadan, irin wannan hali kan kai mutum ga hallaka na har abada.

Bari mu ga wasu misalai a ciki Littafi Mai tsarki, 

“Amma wani mutum mai suna Hananiya da matarsa Safiratu, ya sayar da wata gona mallakarsa, sai ya boye wani abu daga cikin kudin da sanin matarsa, ya kawo sashin kudin kurum ya ajiye a gaban manzanni. Sai Bitrus ya ce, “Kai Hananiya, ta kaka Shaidan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai tsarki karya, ka kuma boye wani abu daga kudin gonar? Kafin ka sayar, ba taka ba ce? Bayan ka sayar kuma, kudin ba halalinka ba ne? Ta kaka ka riya wannan aiki a zuciyarka? Ai, ba mutum ka yi wa karya ba, Allah ka yi wa.” Da jin wannan magana Hananiya ya fadi ya mutu. Duk wadanda suka ji kuwa, matsanancin tsoro ya kama su. Samari suka taso, suka sa shi a likkafani, suka dauke shi suka fitar da shi, suka je suka binne shi. Bayan misalin sa’a uku matarsa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba. Sai Bitrus ya ce mata, “Gaya mini, shin, haka kuka sayar da gonar nan?” Sai ta ce, “eh, haka ne.” Amma Bitrus ya ce mata, “kaka kuka gama baki ku gwada Ruhun Ubangiji? Kin ji tafiyar wadanda suka binne mijinki, har sun iso bakin kofa ma, za su kuwa dauke ki, su fitar da ke.” Nan take, ta fadi a gabansa, ta mutu. Da dai samarin suka shigo, suka iske ta matacciya, suka dauke ta suka fitar da ita, suka binne ta a jikin mijinta. Sai matsanancin tsoro ya kama dukan Ikilisiyyar da kuma dukan wadanda suka ji labarin wadannan abubuwa.” Ayyukan Manzanni 5:1-11. 

karya ba ta da mazauni cikin Ikilisiyya da rayuwar Kirista. Mu yi kokari mu nemi jagorancin Ubangiji cikin komai, ta wuri haka ne za mu samu nasara cikin rayuwarmu. Yesu Almasihu bai koya mana irin wannan hali ba, gama Yesu Kiristi ne hanya da gaskiya da kuma rai. Ba karya ko kadan a cikin rayuwarsa, haka kuma ya kamata mu zama a zamanmu na masu bin sa. Duk makaryaci bawan Ibilis ne, gama a rubuce yake, “Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi da ma tun farko mai kisan kai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa’ad da yake karya, cinikinsa yake yi, don shi makaryaci ne, uban karairayi kuma.” Yahaya 8:44. Ba za ka taba jin dadin rayuwar nan ba idan ka gina komai bisa karya. Ubangiji Allah ba zai taba kaunarka ba. Shi mai gaskiya ne, Mai tsarki Ubangijin masu fadin gaskiya. A wani bangare kake? Domin, “Duk mai so ya more wa zamansa na duniya da alheri, sai ya kame bakinsa daga barna, ya kuma hana shi maganar yaudara.” 1 Bitrus 3:10

 “Saboda haka, sai ku watsar da karya, kowa ya rika fadar gaskiya ga makwabcinsa, gama mu gabobin juna ne.” Afisawa 4:25. Gaskiyar ke nan fa, mu watsar da rayuwar yaudara da fadin karya, mu juyo ga Ubangiji. Gama babu wata fara ko bakar karya, karya daya ce a gaban Ubangiji. Saboda haka, sai mu dauki sabon halin nan da Ubangiji ya nuna mana cikin Yesu Kiristi, don mu ci nasara.

“Kada ku yi wa juna karya, da yake kun yar da halinku na da da ayyukansa, kun dauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.” 1 Kolosiyawa 3:9-10. 

Mu sabunta halayenmu ga tafarkin Ubangiji, mu kuma nemi nufi da jagorancinSa cikin komai da a koyaushe, don mu kasassu ne masu zunubi, amma kaunar Ubangiji Allah kadai ne zai cece mu, shi ya sa ya kamata mu zo gare Shi don neman cin nasara a cikin komai a kowane irin hali da muka tarar da kanmu a ciki don mu samu tsira.

Bari Ubangiji Ya taimake mu, amin.