‘Addu’a ce maganin annoba’
Babban Limamin Masallacin Izala na Kalaba a Jihat Kuros Riba, Ustaz Bashir Salihu Abuga ce addu’a ita ce kadai mafita ga al’ummar Musulmi sai kuma kiyaye dokoki da ka’idoji da addinin Musulunci ya shimfida gare su idan aka samu bullar wata annoba a kasa ko a duniya. Limamin ya bayyana haka ranar Lahadi a Kalaba […]
Masu rigakafin cutar Kurona
Babban Limamin Masallacin Izala na Kalaba a Jihat Kuros Riba, Ustaz Bashir Salihu Abuga ce addu’a ita ce kadai mafita ga al’ummar Musulmi sai kuma kiyaye dokoki da ka’idoji da addinin Musulunci ya shimfida gare su idan aka samu bullar wata annoba a kasa ko a duniya.
Limamin ya bayyana haka ranar Lahadi a Kalaba lokacin da yake amsa tambayoyIn wakilin Aminiya kan bullar cutar Kurona da ta addabi duniya jim kadan da kammala wa’azin kungiyar na jiha da aka yi.
Sheikh Salihu Abuga ya ce “Idan wata annoba ta samu a kasa ko ta shafi duniya babu abin da ya fi dacewa ga Musulmi ya yi face wanda ke cikin wurin da annobar ta bulla kada ya fita yayin da wanda ke wajen garin kuma kada ya shiga, mataki na farko ke nan da Musulunci ya tanada na hana yada cutar.”
Game da me ya kamata Musulmi ya rika yi musamman yadda cutar ta Kurona ke neman ta karade duniya sai ya ce “Addu’a safe da yamma ya kamata Musulmi su rika yi.”
Kan wanke hannu da sabulu ko kin masabaha da juna don gudun kamuwa da cutar, limamin cewa ya yi “Ai musulmi koyaushe addininsa ya karantar da shi tsabta tun daga alwala akalla sau biya a kowace rana idan zai yi Sallah da kuma wanke hannu kafin ya ci abinci da kuma bayan an ci abincin,”