Addu’a kawai ba za ta kawo gyara ba

A kwanakin baya na bayyana wasu daga cikin dalilan da ba a cika jina a kafafen watsa labarai musamman na kasashen waje ba. Ina so jama’a su fahimci cewa ba fa surutu kawai nake yi a matsayina na shugaban kungiyar Rundunar Adalci ta kasa ba. Nakan rubuta takardar koke-koke ga hukumomin yaki da cin hanci […]

Addu’a kawai ba za ta kawo gyara ba
Addu’a kawai ba za ta kawo gyara ba

A kwanakin baya na bayyana wasu daga cikin dalilan da ba a cika jina a kafafen watsa labarai musamman na kasashen waje ba. Ina so jama’a su fahimci cewa ba fa surutu kawai nake yi a matsayina na shugaban kungiyar Rundunar Adalci ta kasa ba. Nakan rubuta takardar koke-koke ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa kan duk abin da nake da yakinin an yi rashin gaskiya a cikinsa. Kuma a irin wannan gwagwarmaya na sha haduwa da barazana iri-iri har da ta rayuwata, Allah ne Yake tsare ni.
 Alhamdulillah! Ko a baya-bayan nan lokacin da muka kai karar kananan hukumomi 44 na Jihar Kano zuwa ga EFCC a Abuja, a kan Naira biliyan 202 da shugabannin kananan hukumomin suka karbo cikin shekara uku, amma babu koda kashi daya cikin uku na kudin a kasa da za a gani. Bayan EFCC sun kammala bincikensu, suka fara kakkame shugabannin kananan hukumomin, nan da nan aka je, aka yi belinsu, har tsawon wata shida ba a dago maganar ba. Ni da kaina na je na samu Ministan Shari’a, ni da shi a ofishinsa da ke Abuja, na ba shi takarda a rubuce da sa hannuna, kunshe da cikakken bayanin abin da ya faru, na yi kira gare shi ya kafa kwamiti ya binciki kukan namu, ya amsa ya ce zai yi duk abin da ya kamata domin tabbatar da adalci.
 Amma har yau bai yi komai a kai ba, kamar hadin baki. Duk kasar nan kowa ya san da maganar, amma hatta ’yan uwana da aka yi wa satar ba su damu su yi komai a kai ba, balle kafafen watsa labarai. Kamar dai yadda sama da Naira tiriliyan daya da biliyan 700 na tallafin mai da aka sace mana, amma Ministan Shari’a bai yi komai a kai ba, ’yan uwana da aka yi wa satar ba su yi komai a kai ba, kungiyar kwadago ta NLC sun yi mana shan kai, har aka yi karin kudin man daga Naira 65 zuwa Naira 97. Sannan NLC din ta ki yin katabus a kan wancan kudin da aka sace mana da sunan tallafi mai. Ba zan bar maganar ta mutu ba tare da an kwato dukkan kudin ba, har da ma wadanda aka sace kafin su, insha Allah. Musamman kasancewar ni ne jagoran hada kan duk kungiyoyin da muka hadu a gidan Malam Aminu Kano, MAMBAYYA HOUSE, inda na gabatar da kasida a kan yin zanga-zangar lumana. Kamar yadda AIT ta yi ta nunawa, duk duniya ta gani. Wacce ta kasance irinta ta farko da aka taba yi a Najeriya da hadin kan kowa da kowa, Kiristoci da Musulmi da marasa addini na kowane bangaren kasar nan.
Muna sane da kasancewar ’yan kwadago (NLC) suna daga cikin mutane miliyan daya cikin mu miliyan 167 da suke rabe kashi 70 cikin 100 na arzikin Najeriya, yayin da mu miliyan 166 aka bar mu da kashi 30 cikin 100 kacal. Duk da haka, suke daka mana wawaso cikin kashi 30 din namu, saboda tsabar zalunci da tsabar raunin talakawan da ake zalunta.
Har sai yaushe hankalinmu zai komo jikinmu, tunaninmu ya yi saiti, mu manta da kungiyar kwadago ta NLC, mu hadu mu-ya-mu, mu fara tsara yadda za mu bi kadin kudadenmu da aka wawashe mana? Da diyyar rayukan da suka salwanta ba tare da hukuncin kotu ba. Mun ji bayanin tsohuwar Ministan Kudi tana tabbatar da cewa gwamnatin Jonathan ta gaji Dala biliyan 67 a Asusun Ajiyar Waje, amma gwamnatin ta ce Naira biliyan 47 ne, su din ma ba a ga abin da aka yi da su ba.  Ina NLC mai hada kai da gwamnati a kara kudin mai, a karya mana zanga- zangarmu ta lumana, ta daukacin talakawan Najeriya marasa albashi da wadanda aka rufe kamfanoni da masana’antun da suke aiki?
Ga shi tsohon ma’aikacin fensho da ya saci Naira biliyan 27, kotu ta daure shi shekara biyu ko tarar Naira dubu 750, yanzu haka yana yawo ko’ina. Ina shugabannin NLC masu yaudararmu? Irin wadannan dokokin tunda ba na Allah ba ne, dole mu rusa su, mu maye gurbinsu da tsantsar adalci a kan kowa da kowa.  
Wannan shi ne kalubalen da ke kan duk wanda aka zalunta a nan kasar. Allah ba Ya canja wa mutane, sai mutane sun canja wa kansu da kansu. Kamar yadda muke gani ko jin labarin abubuwan da suke faruwa a wasu kasashen duniya yanzu. Ko mun manta da yadda talakawa suka kori Turawan mulkin mallaka na Ingila daga Najeriya, har aka samu mulkin kai da yadda aka kakkabe hannayen sarakuna daga mallakar kasa da izinin ginawa da kurkuku da kotu da alkalai da ’yan sanda da karbar haraji da jangali, komai ya koma hannun talakawa, daga kasa har sama.
Koda ake cewa, juyin juya-hali yana farawa daga mutum daya, amma ba aikin mutum daya ba ne shi kadai. Kowa ya san da haka. Misali, tafiya ce ta mil 100 da ake bukatar mutum 100, su je su yi aikin kwana 100, idan suka kammala kowannensu zai samu Naira miliyan 100. Amma ana fara tafiya ko mil daya ba a yi ba, sai wasu suka ja birki, saboda an ba su sabulu da ashana da Naira 50 ko turmin atamfa da farar shadda yadi biyar zuwa ’yan dubban nairori da ba su wuce dubu biyar zuwa dubu goma ba, domin su bata tafiyar a kafafen watsa labarai. Da kuma wasu ma’aikatan kafafen watsa labaran da ake zargi da hadin kai, idan aka ba su ambulan mai launin kasa da haka-da-haka kafin a je inda ake so, idan jagoran ya waiwaya da kyar zai ga mutum uku ko biyar. Ta yaya mutum shida za su iya yin aikin mutum 100 a cikin adadin kwanakin da aka kebe musu na kwana 100 kafin a gama shi? Ka ji inda gizo yake yin sakar.
Abu na karshe shi ne saba wa Allah, musamman zina da luwadi da madigo da wasu suka camfa idan sun yi za su zama masu mulki ko sarauta ko dukiya. Har sun yarda da lakabin cinye zunubi. Sun manta, ko babu ruwansu da gargadin da Allah (SWT) Ya yi cikin Alkur’ani Mai girma cewa kada a kusanci zina da Hadisin Annabi (SAW) da ya ce: matukar al’umma suna yin zina (balle luwadi da madigo), Allah zai saukar da annobar mutuwa a cikinsu. Ga shi nan kowa yana gani; masu yi sun ki dainawa har ma suna cewa a bar su, su auri jinsinsu-Wa’iyazu Billah! Ga tauye ma’auni ko algus da rashin cika alkawari da rashin bayar da zakka da rashin yin shari’a ta adalci, kamar yadda take a cikin Littafin Allah. Komai addu’ar masu cewa a yi addu’a, babu abin da zai gyaru sai an daina wadannan laifuffuka.
Alhaji Abdulkarim daiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya
08060116666, 08023106666

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50