Addu’a makamin mumini (1)
Allah (S.W.T) Ya ce: “Wa’iza sa’alaka Ibadi Anni fa inni karibun Ujibu da’awatad da’i iza da’ani, fal yastajibu li wal u’uminu bi la’allahum yarshidun”. 2: (186). Kuma an karbo daga Sayyadina Aliyu (Karramallahu wajahahu), Allah (S.W.T) ya ce: “Addu’a makamin mumini ce, kuma ginshikin addini ce, kuma hasken sama da kasa ce”. Hakim ne ya […]
Allah (S.W.T) Ya ce: “Wa’iza sa’alaka Ibadi Anni fa inni karibun Ujibu da’awatad da’i iza da’ani, fal yastajibu li wal u’uminu bi la’allahum yarshidun”. 2: (186).
Kuma an karbo daga Sayyadina Aliyu (Karramallahu wajahahu), Allah (S.W.T) ya ce: “Addu’a makamin mumini ce, kuma ginshikin addini ce, kuma hasken sama da kasa ce”. Hakim ne ya ruwaito shi a cikin mustadrik.
ALBARKAR ADDU’A
Allah (S.W.T) ya ce: “Kul ma ya’aba’u bikum rabbi laula du’a’ukum” suratul furkan, 77.
Kuma Allah (S.W.T) ya ce: ‘Wa iza sa’alaka Ibadi Anni Fa’inni karibun ujibu da’awatid da’i iza da’ani, fal yastajibu li wal yuminu bi la’allakum yarshidun”
Haka kuma ita dai addu’a shiriya ce kuma dalili ce ta kaskantar da kan bawa ga ubangijinsa da kuma imaninsa, yana daga rahamar Allah ga bayinsa, in sun roke shi zai amsa musu.
Manzon Allah (S.W.A) ya ce: “Hakika ubangijinku rayayye ne mai girma ba ya bari daga bawansa idan ya daga hannayensa izuwa gare shi ya dawo da su a banza, tababbu” Ahmad da Dawud da Turmizi suka ruwaito lafazin nasa.
Ya kyautatu kuma ya wajaba ga bawa mai ikhlasi ga Allah da kuma bawa abin zalunta, da ya yi kaunar adalcin Allah da RahamarSa, hakika Allah zai gaggauta amsawa kuma Ya juyar da dukkan zalunci ga barinsa, kuma ya yi rahama musu da kudirarSa, domin shi Allah mai iko ne akan dukkan komai, kuma macancanci ne da asawa kuma mai taimako ga dukkan wanda aka zalunta.
Kuma hakika ana juyar da kaddara (hukunci) da albarkar addu’a, domin fadin Manzon Allah (S.A.W): “Ba abinda yake juyar da kaddara sai addu’a kuma babu abinda yake karawa cikin rayuwa sai bin Allah” Sahihu Jami’i 7564. Ihya’u Ulumideen . Imam Gazali
To ya wajaba akan bawa mai rokon Ubangijinsa da ya kasan ce mai sakankancewa da karbawa, kuma ya yawaita daga addu’ar.
An karbo daga Sayyidina Mu’azu (R.A.) yace: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Hanzari baya amfanarwa daga kaddara sai dai cewa addu’a tana amfanarwa daga abinda ya sauka da kuma abinda bai sauka ba, saboda haka na horeku da yin addu’a ya ku bayin Allah”
Ahmad da kabarani suka ruwaito.
Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ku roki Allah kuma masu sakankancewa da amsawa, ku sani cewa hakika Allah baya karbar addu’a daga zuciyar rafkanan ne, shagalalle”. Silsilatul – Ahadisis – Sahiha na Albani 594.
Sakankancewa
Yana nufin bawa ya rinka rokon ubangijin da gaskiya, kuma ya kasance babu mafaka babu matsera daga Allah sai zuwa gare shi (S.W.T).
Daga dan Abbas (R.A) daga Annabi (S.A.W) ya ce: “Addu’o’i biyar ana amsawa garesu, addu’ar wanda aka zalunta har sai an taimake shi, addu’ar mai hajji har sai ya dawo, addu’ar mai jihadi har sai ya komo gida ya zauna, addu’ar mara lafiya har sai ya warke, addu;ar dan uwa ga dan uwansa a bayan fage” (ga’ibi) wanda baya nan. Baihaki ya ruwaito.
Ya wajaba akan wanda zai roki Allah da ya saukaka addu’ar kuma ya cikata da salati ga Manzon Allah (S.A.W) don kada a tsare addu’ar.
Hakika Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Dukkan addu’a abar tsarewa ce har sai an yi salati ga Annabi Muhammad (S.A.W) Sahihul Jami’i na Albaniy 4/4399.
Bawa ya kaskantar da kai ya yi khushu’i a cikin addu’ar kuma ya kaunaci Allah, kuma ya roki Allah roko na miskini rarrauna. Hakika ana jarrabar bawa ya yin addu’a ba za a amsa masa ba, to kada abincinsa ya kasance haramun ne ko ma zauninsa ko abin sawarsa in duk haramun ne to ta yaya za’a amsa masa, to tuba ya wajaba akansa da kuma tsarkakewa ga Allah a farko.
Kuma hakika bawa ya kasance na gari, Allah ya a jiye masa addu’arsa domin ranar lahira don mizanin kyakkyawan aikinsa ya yi nauyi kuma a gafarta masa mummunan aikinsa, saboda abinda sa’idul khudiriyyu ya ruwaito ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Babu daga musulmi da zai yi addu’a da wata addu’a babu wani zunubi cikinta ko kuma yanke zumunci, face sai Allah ya ba shi uku uku da ita, kodai ya gaggauta masa addu’arsa, ko kuma ya jinkirta masa ladanta, ko kuma ya kame wani mummuna ga barinsa da misalinta, sai sahabbai suka ce idan muka yawaita fa, sai Annabi (S.A.W) ya ce “Sai Allah ya yawaita” Ahmad ne ya ruwaito shi.
An rawaito cewa: idan ranar kiyama ta kasance ‘yan Aljanna Allah ya yi ni’ima a gare su da ni’imominta. Kuma wannan bawa na gari zai kasan ce a cikin katangunsa da kuma tsakanin ‘yan uwansa da masoyansa (Sahihai) kuma a gare su akwai hasken ni’ima, kuma daga gefensa ga mala’iku suna kewayawa, kuma hakika ya sami daga huril’in, kuma shi yana daga masu arzuki, kawai sai ga mala’iku suna zuwa da kyaututtuka da baiwoyi, sai bawan ya ce, mene ne wannan? Sai su ce: shin baka kasance kana rokon Allah a duniya ba? Wannan addu’ar ka ce wacce ka kasance kana rokonsa, hakika ya ajiyeta gare ka a cikin wannan ni’ima mai girma.
kuma hakika an ambata ga Abdussalam dan mudi’i cewa hakika wani mutum bala’i ya same shi, kuma ya yi addu’a sai aka jinkirta amsawa a gare shi, sai ya ce: labari ya isar min hakika Allah (S.A.T) yana cewa: kaka zan rahamsheku daga binda da shi Nayiwa bayiNa yi rahama.
Mustdriku Sahihaini.
Kuma Manzon Allah (S.A.W) yace: “Wanda duk aka bude masa kofar addu’a daga cikinku to an bude masa kofifin rahama. don Abi Shaibata ne ya ruwaito.
Za mu cigaba