Addu’a makamin mumini (2)

Domin cewa addu’a ibada ce ga Allah mai rahama da girma da buwaya, kuma dalilin furuci ne da kauna da tabbatarwa da dacewa, hakika Allah (S.W.T) shi ne gaskiya kuma shi ne wanda a hannun kudurarsa komai yake, domin cewa shi ne mahaliccin komai.  Daga Nu’umana dan Bashiru (R.A), ya ce Manzon Allah (S.A.W) ya […]

Addu’a makamin mumini (2)
Addu’a makamin mumini (2)

Domin cewa addu’a ibada ce ga Allah mai rahama da girma da buwaya, kuma dalilin furuci ne da kauna da tabbatarwa da dacewa, hakika Allah (S.W.T) shi ne gaskiya kuma shi ne wanda a hannun kudurarsa komai yake, domin cewa shi ne mahaliccin komai. 

Daga Nu’umana dan Bashiru (R.A), ya ce Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Addu’a ita ibada ce” dan Hibbana ya fitar da shi a cikin sahihunsa.
Daga Abu Huraira (R.A) ya ce; Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Wanda baya rokon Allah, Allah zai yi fushi da shi. Dawud da Tirmizi ne suka ruwaito. Ihya’u Ulumedden, Imam Gazali.
kuma hakika duk wanda baya rokon Allah, to, shi mai girman kai ne, kuma kamar cewa shi ya aminta da takalar Allah, kuma kamar cewa al’amarinsa a hannunsa yake, alhalin shi hakika bai mallaki wani abu daga al’amarinsa ba, al’amari yana ga Allah tun gabanin da kuma bayan, Allah Ya yi gaskiya. Allah Acikin LittafinSa mai tsarki Ya na cewa,
“UD’UNI ASTAJIB LAKUM INNALLAZINA YASTAKBIRUNA AN IBADATI SAYADKHULUNA JAHANNAMA DAKHILUN”
Suratul Gafir aya ta 60.
Allah Yana fushi da kai idan kabar rokonsa, shi ko dan Adam yana fushi ya yin da ake tambayarsa, sai cewa Allah shi ne mafi jinkai ga bawansa fiye da uwa ga danta, to kaga albarkar addu;a ba mai riskarta sai wasu bayi ga Allah masu tsoronsa, ita addu;a taska ce da bata girgiza har abada kuma makami ce da baya dakushewa.
Addu’a wata babbar abu ce cikin shari’ar Musulunci. Haka kuma, ibada ce daga cikin ibadojin da Allah ya umurci bayinsa da su aikata. Daga cikin ibadodinda Allah ya umurci bayinsa da yi babu kamar du’a’i daraja da daukaka a wajen Allah. Fada’ilu du’ai
An ruwaito hadisai da yawa da suka bayyanar da irin karfin addu’a da matsayinta cikin addinin Musulunci. A hadisin da abahuraira ya ruwaito, Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
“Babu wani Abu da ya fi daukaka a wajen Allah fiye da addu’a”
A wata riwaya kuwa Manzon Allah (S.A.W) cewa ya yi: “Mafi daukaka daga ibadoji ita ce addu’a” A takaice hadisin Nu’umanu dan Bashiru yace Annabi (S.A.W) ya ce:
“Hakika addu’a ibada ce, sai ya karanta ayar: “ku kiraye ni in karba muku kiran ku”
Babu shakka, Allah ya fada a cikin littafinsa cewa, duk bawan da ba ya yin du’ai babu ruwan Allah da shi. Abin da ake nufi a nan shi ne, Allah ba ya kula da al’amarin wanda duk ba ya rokonsa. Wanda duk Allah ba ya kula dashi, yana cikin musiba babba da halaka, ayar na cewa:

“Ka ce, ubangijina ba ya kula da ku in ba domin addu’arku ba. To lalle ne, kun karyata saboda haka al’amarin za ya zama malizimci”.
Bugu da kari Alkur’ani ya bayyana muna cewa, rashin yin addu’a girman kai ne ga barin yin ibada. Don haka, wanda ba ya addu’a mutakabbiri ne, mutakabbiranci kuwa mai kai mai shi ga jahannama ne, kamar yadda mahaliccin halittu ke cewa.
“Ka ce, ubangiji ba ya kula da ku in ba domin addu;arku ba. To alle ne kun karya ta saboda haka al’amarin za ya zama malizinci”
“Kuma ubangiji ya ce ku kira ni in karba, lalle wadanda ke kangara ga barin bauta mini, za su shiga jahannama suna kaskantattu”
“Babu wani uzuri ko riga kafin da zai yi amfani ga kawar da kaddara. Ita addu’a tana amfani ga abubuwan da aka sauko da wadanda ba a sauko ba. Hakika ana sauko da bala’i sai ya gamu da addu’a sai addu’a ta dafe shi ta murtuke shi har ranar tashin kiyama”
Haka kuma, an samu hadisin da Salmanul Farisi (R.A.) ya ruwaito cewa, Manzon Allah (S.W.A) ya ce:
“Babu abin da ke mayar da abin da aka kaddaro sai addu’a.
Ihya’u Ulumiddeen Imam Gazali
A takaice, wadannan hadisan na karantar da mu cewa kaddara ba ta da magani face addu’a. Wanda duk bai kula da addu’a ba ako yaushe, to, shi ya kasance naman kaddara ne, Allah ya tsare mu.
Da yake mun riga mun ga irin muhimmancin addu’a da irin karfinta abin da ya rage mana shi ne, sanin abubuwan da ake son a yi cikin addu’a da wurarenda aka fi karbar addu’a da abubuwanda ake so ga wanda zai yi addu;a da yadda za’a yi addu’a ita kanta da dai sauransu. Wa dannan su ne makasudin wannan rubuta nawa. Yanzu sai mai karatu ya biyo ya ganewa idanunsa yadda abubuwan suke a hadisan Annabi (S.A.W).

ABUBUWAN DA AKA SUNNANTA YI GA DU’A’I DOMIN SAMUN IJABA
Kasancewar addu’a wani yanki ne daga ibada, wadda Allah ya ambata a cikin buwayayyen littafinSa, Manzon Allah (S.A.W) ya karfafa a cikin hadisansa. Akwai abubuwan da suka tusgo daga manzon Allah (S.A.W) da ake gabatarwa, a lokacin du’a’i. kuma Wadannan abubuwan sunna ne, domin samun tabbacin da aka yi na aikata su daga Annabin rahama (S.A.W). idan har an ruwaito abubuwa da Annabi (S.A.W) yake yi idan yana ganawa da ubangijinsa a kan bukatocinsa, ashe ke nan duk wani mai bukatar ya gaya wa Allah bukatunsa akarba masa dole yayi koyi da tafarkin Annabi (S.A.W).