Addu’ar dogara ga kiyayewar Ubangiji
“Ubangiji ne haskena da cetona, Ba zan ji tsoron kowa ba. Ubangiji Yana kiyaye ni daga dukan hadari, Ba zan ji tsoro ba.” – Zabura 27:1. Ya Allah, Ka ji kukana, Ka ji addu’ata! Sa’ar da nake nesa da gida, zuciyata ta karaya, zan yi kira gare ka! Ka kai ni lafiyayyiyar mafaka. Kai ne […]
“Ubangiji ne haskena da cetona, Ba zan ji tsoron kowa ba. Ubangiji Yana kiyaye ni daga dukan hadari, Ba zan ji tsoro ba.” – Zabura 27:1.
Ya Allah, Ka ji kukana, Ka ji addu’ata!
Sa’ar da nake nesa da gida, zuciyata ta karaya, zan yi kira gare ka! Ka kai ni lafiyayyiyar mafaka. Kai ne kariyata mai karfi da take kiyaye ni daga makiyana. Ka yarda in zauna a alfarwarKa dukan kwanakin raina, Ka yarda in samu zaman lafiya a karkashin fika-fikanka. Ya Allah! Ka ji alkawarina, Ka kuwa ba ni abin da ya dace, tare da wadanda suke daukaka Ka. Ka kara wa sarki tsawon rai, Ka sa ya rayu dukan lokaci! Ka sa ya yi mulki har abada a gabanKa, ya Allah, Ka tsare shi da madauwamiyar kaunarKa da amincinKa. Don haka zan yi ta rera wakar yabonKa kullum, a sa’ar da nake mika maKa abin da na alkawarta. Duk wanda ya je wurin Madaukaki Zai zauna lafiya, Duk wanda yake zaune a inuwar Mai Iko Dukka, ya iya ce wa Ubangiji, “Kai ne kāriyata, da mai kiyaye ni! Kai ne Allahna, a gare Ka nake dogara!” Hakika zai kiyaye ka Daga dukan hadarurrukan da ka boye, Daga kuma dukan mugayen cututtuka. Zai rufe ka da fika-fikanSa, Za ka zauna lafiya a karkashinsu. AmincinSa zai tsare ka, Ya kiyaye ka ba za ka ji tsoron hadarurruka da dare ba, Ko fadawar da za a yi maka da rana, ko annobar da take aukowa da dare, Ko mugayen da suke kisa da tsakar rana. Mutum dubu za su fadi daura da kai, Dubu goma kuma za su fadi dama da kai, Amma kai, ba za a cuce ka ba. Da idonka za ka duba, Ka ga yadda ake hukunta wa mugaye. Domin ka dauka Ubangiji Yake kiyaye ka, Madaukaki ne Yake tsaronka, To, ba bala’in da zai same ka, Ba za a yi wa gidanka aikin karfi da yaji ba. Allah zai sa mala’ikunSa su lura da kai, Za su kiyaye ka duk inda za ka tafi. Za su dauke ka a hannuwansu, Don kada ka buga kafarka a dutse. Za ka tattake zakoki da macizai, Za ka tattake zakoki masu zafin rai Da macizai masu dafi. Allah Ya ce, “Zan ceci wadanda suke kaunaTa, Zan kiyaye wadanda suka san Ni. Sa’ar da suka kira gare Ni, zan amsa musu, Zan kasance tare da su sa’ar da suke shan wahala, Zan cece su in girmama su. Zan ba su tsawon rai lada, Hakika kuwa zan cece su.” Na duba wajen duwatsu, Daga ina taimakona zai zo? Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda Ya yi sama da kasa. Ba zai bar ka ka fadi ba, Makiyayinka, ba zai yi barci ba! Makiyayin Isra’ila, Ba ya gyangyadi ko barci! Ubangiji zai lura da kai, Yana kusa da kai domin Ya kiyaye ka. Ba za ka sha rana ba, Ko farin wata da dare. Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan hadari, Zai sa ka zauna lafiya. Zai kiyaye shigarka da fitarka, Tun daga yanzu har abada. Ubangiji ne haskena da cetona, Ba zan ji tsoron kowa ba.
Ubangiji Yana kiyaye ni daga dukan hadari, Ba zan ji tsoro ba. Sa’ar da mugaye suka tasar mini, Suna kokari su kashe ni, Za su yi tuntube su fadi. Ko da rundunar mayaka ta kewaye ni, ba zan ji tsoro ba. Ko da magabtana sun tasar mini, zan dogara ga Allah. Abu guda nake roko a wurin Ubangiji, abu daya kadai nake bukata, shi ne in zauna a masujadar Ubangiji, in yi ta al’ajabin alherinSa dukan kwanakin raina,
In roki biyarwarSa a can. A lokatan wahala zai kiyaye ni a inuwarSa, zai kiyaye ni lafiya a haikalinSa, zai dora ni a kan dutse mai tsawo, Ya kiyaye ni. Ta haka zan ci nasara a kan magabtana da suke kewaye da ni. Da sowar farin ciki mai yawa zan mika sadakoki a haikalinSa! Zan rera waka, in yabi Ubangiji! Ka ji ni, ya Ubangiji! Sa’ar da na na yi kira gare ka! Ka yi mini jinkai Ka amsa mini! Ka ce, “Zo wuriNa,” zan kuwa zo gare Ka, ya Ubangiji! Kada Ka boye mini fuskarKa, ya Ubangiji! Kada ka yi fushi da ni, kada kuwa Ka kori bawanKa. Kai ne Kake taimakona, tun dama, kada Ka bar ni, kada Ka yashe ni, ya Allahna, Mai Cetona! Mai yiwuwa ne ubana da uwata su yashe ni, amma Ubangiji zai lura da ni. Ka koya mini abin da ya kamata in yi, ya Ubangiji! Ka bi da ni kan lafiyayyiyar hanya, domin ina da magabta da yawa. Kada Ka bar ni a hannun magabtana, wadanda suke fada mini da karairayi da kurari. Hakika zan rayu domin in ga alherin Ubangiji da zai yi wa jama’arSa. Ka dogara ga Ubangiji!
Ka yi imani, kada ka karaya.
Ka dogara ga Ubangiji!
Zabura 61, 91, 121.