Adebayor ya kuma Crystal Palace

Shahararren dan kwallon Togo Emmanuel Adebayor ya koma kulob din Crystal Palace na Ingila don cigaba da wasa.FRahotanni sun nuna dan kwallon ya koma can ne a matsayin kashin kansa tun bayan da kwantaraginsa ta kare da kulob din Tottenham na Ingila.  Haka kuma yarjejeniyar za ta kasance ne zuwa karshen kakar wasa ta bana, […]

Adebayor ya kuma Crystal Palace
Adebayor ya kuma Crystal Palace

Shahararren dan kwallon Togo Emmanuel Adebayor ya koma kulob din Crystal Palace na Ingila don cigaba da wasa.F
Rahotanni sun nuna dan kwallon ya koma can ne a matsayin kashin kansa tun bayan da kwantaraginsa ta kare da kulob din Tottenham na Ingila.  Haka kuma yarjejeniyar za ta kasance ne zuwa karshen kakar wasa ta bana, inda watakila daga nan ya sake kulla sabuwar yayrjejeniya da kulob din a matsayin na dindindin.
Adebayor, wanda ya taba yi wa kulob din Arsenal da Manchester City da Tottenham kwallo a Ingila, ya zura kwallaye 94 a tsawon lokacin da ya yi a gasar rukunin firimiya ta Ingila.  Ya kuma taba yi wa kulob din Real Madrid na Sifen kwallo a matsayin na aro.
Kawo yanzu kulob din Palace ne na 11 a teburin firimiya ta Ingila bayan ta hada maki 31. Adebayor dai ya kulla yarjejeniya da kulob din ne zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa