Adebayor zai raba wa mabukata takalmansa

Shahararren dan kwallon Togo da yanzu haka yake kwallo a kulob din Tottenham da ke Ingila ya bayar da sanarwar raba takalmansa da suka hada da na kwallo da kuma na gayu ga mabukata.dan kwallon ya bayyana haka ne a karshen makon jiya a kafar sadarwarsa ta Intenet  inda ya ce “Kwanan nan zan raba […]

Adebayor zai raba wa mabukata takalmansa

Wasu daga cikin takalman da Emmanuel Adebayor zai raba wa mabukataShahararren dan kwallon Togo da yanzu haka yake kwallo a kulob din Tottenham da ke Ingila ya bayar da sanarwar raba takalmansa da suka hada da na kwallo da kuma na gayu ga mabukata.
dan kwallon ya bayyana haka ne a karshen makon jiya a kafar sadarwarsa ta Intenet  inda ya ce “Kwanan nan zan raba takalmana masu tsada ga mabukata”.
Sai dai bayanin nasa bai ambaci inda zai yi wannan rabo ba walau a Ingila ne ko kuma a yankin Afirka musamman kasar haihuwarsa Togo.