Adeniyi Adeyemi: An kama mutumin da ake zargi da kafa hukumar bogi a Najeriya
Jami’an tsaro a ranar Talata sun kama mutumin nan da ake zargi da ƙirƙira wata hukuma ta bogi a Najeriya kuma ya naɗa kansa a matsayin Darakta Janar. An kama Adeniyi Adeyemi wanda ke iƙirarin cewa shi ne shugaban hukumar ba da shawara kan haɓaka kasuwanci da ƙasashen ƙetare (PFIPC) bayan makonni ana ce-ce-ku-ce kan […]
Jami’an tsaro a ranar Talata sun kama mutumin nan da ake zargi da ƙirƙira wata hukuma ta bogi a Najeriya kuma ya naɗa kansa a matsayin Darakta Janar.
An kama Adeniyi Adeyemi wanda ke iƙirarin cewa shi ne shugaban hukumar ba da shawara kan haɓaka kasuwanci da ƙasashen ƙetare (PFIPC) bayan makonni ana ce-ce-ku-ce kan ɗambarwar.
- An kammala gasar tseren dawakai ta farko a Masarautar Jama’a
- Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 221 cikin watanni shida a Najeriya
Mahukunta sun cafke Adeyemi ne a maɓoyarsa da ke Jihar Osun, kuma ana sa ran za a kai shi hedikwatar rundunar ’yan sanda da ke Abuja domin ci gaba da bincike da kuma shirya gurfanar da shi a gaban kotu.
Tun a ranar Talata ce Mai Shari’a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya ya ba da umarnin kama shi.
Sai dai Adeyemi bai bayyana a gaban kotun ba, duk da cewa gwamnati ta ce an riga an miƙa masa sammaci.
Lauyan Gwamnatin Tarayya, Wisdom Madaki, ya shaida wa kotun cewa wannan ba shi ne karo na farko da wanda ake zargin ya ƙi halartar kotun ba, domin an riga an ɗage shari’ar har sau biyar saboda rashin zuwansa domin a gurfanar da shi.
Saboda haka ne ya roƙi kotun ta bayar da sammacin da zai bai wa jami’an tsaro damar kamo Adeyemi tare da gabatar da shi a gaban kotu a ranar da za a ci gaba da sauraron shari’ar.