Ado Ahmad Gidan Dabino da na sani a jiya da yau
A jibi Lahadi ce ’yan uwa da abokai, musamman marubuta za su taru a Gidan Mumbayya Kano, domin bikin taya marubuci Ado Ahmad Gidan Dabino murnar samun lambar yabo ta kasa (MON) da kuma taya shi murnar cika shekara 50 a duniya. Dalili ke nan shi ma marubuci, dANJUMA KATSINA 08035904408 ya bijiro da wannan […]
A jibi Lahadi ce ’yan uwa da abokai, musamman marubuta za su taru a Gidan Mumbayya Kano, domin bikin taya marubuci Ado Ahmad Gidan Dabino murnar samun lambar yabo ta kasa (MON) da kuma taya shi murnar cika shekara 50 a duniya. Dalili ke nan shi ma marubuci, dANJUMA KATSINA 08035904408 ya bijiro da wannan tsokacin dangane da shi:
Na san Ado Ahmad Gidan Dabino tun cikin 1992, lokacin ina Editan mujallar Gwagwarmaya, ina kuma dalibta. Lokacin an fara muhawara a kan rubutun Adabin Kasuwar Kano a jaridar Nasiha, wadda marigayi Janar ’Yar-aduwa ke wallafawa.
A lokacin jaridu ku kadai ke gare mu na Hausa, wadanda ke karade kasar nan. Su ne Gaskiya Ta Fi Kwabo, Al-mizan sai Nasiha. Sai kuma mujallu, su ma uku; Rana, Hantsi sai Gwagwarmaya, wadda nake editanta.
Mujallar tana sabuwa, lokacin an kafa ta don yaki da zalunci da kuma yada Musulunci, don haka aka sanya mata suna Gwagwarmaya. ’Yar uwa ce ga jaridar Al-mizan amma aka tsara za ta rika bincike da bayyana al’amura ne baro-baro, yayin da Al-mizan kan kawo labarai a kan abin da ke faruwa.
A fitowar mujallar ta goma, na rubuta wata wasika mai taken ‘Zuwa Ga Marubutan Soyayya.’ Wannan wasika ta tayi tsananin tada kura ga wadannan marubuta. Akwatin gidan wayarmu ya cika taf da wasikun kalubale da kuma na kuma goyon baya a kan wannan wasika tawa.
Nan muka fahimci tasirin marubutanmu ga wannan al’umma tamu. Rubutun ya haifar da abubuwa da yawa da suka zama tarihi. A harkar adabi, za su tabbata cikin tarihin har abada, wanda har binciken kundin digiri na daya da na biyu da na uku an yi da yawa a kan wannan muhawara.
A rubutun nawa, hoton da na yi amfani da shi, bangon littafin da Ado Ahmad ya rubuta ne. Mun yi taro na editocin mujallar, aka zartar da cewa in je Kano in gano marubutan, in zanta da su. Aka jera mani sunayensu kamar haka: Ado Ahmad Gidan Dabino, dan’azumi Baba, marubucin So Marurun Zuciya, Bala Anas Babinlata da Hamisu Makwarari.
A Kano, wanda nan da nan aka ce ga inda zan gan shi, shi ne Ado; ko a lokacin yana da ofis. Zan tuna, na iske shi gindin besfa, yana cin wake da shinkafa; wata yarinya ta yi kerere nesa da shi, tana jiran ya gama ya ba ta kwanon.
Bayan mun gaisa, na fada masa abin da ya kawo ni. Sai ya ce, “a sai ka fara da ni ko?” Kafin mu fara aiki, mun tattauna da Ado kuma ya dauke ni bisa besfa dinsa, ya yawata da ni wajen marubuta. Ina jin ta bakinsu a kan ra’ayinsu da matsayarsu a kan rubutun da suke kuma shi ya kai ni tasha.
Mun buga hirarmu da Ado Ahmad a fitowarmu ta 11, da taken ‘Ba Laifinmu Ba Ne, wanda hirar ta karkare a mujallar fitowa ta 13. Ina jin ita ce hira ta farko da aka fara yi da Ado a mujjalla.
Wannan shi ne asalin kullewar mutumcinmu da Ado har zuwa yanzu. Duk lokacin da za ka samu Ado, tunaninsa rubutu ne. Daga fahimtata da shi da na yi, ya kasa ajiye komai saboda kullum yana zirga-zirga wajen tarukan marubuta, wanda zai yi amfani da kudinsa da lokacinsa da ya kamata ya zauna ya nemi kudi, shi yana wajen taro na marubuta.
Kullum yana karfafa wa marubuta masu tasowa, don su hau layin rubutu kuma ya fuskanci kowace matsala, daga ya gwada yadda zama marubuci kuma madabba’i kuma mai sayarwa.
Duk a marubutan nan, ba wanda ya bayar da lokacinsa sukutum a kan yadawa da watsa harkar adabin Hausa kamar Ado. Yana da basira ta iya tsara hanyoyin da zai iya samun kudi amma zirga-zirgar yawon rubutu ta hana shi.
In ya dan ji aljifunsa da ’yar tsaba, maimakon ya tattatala, sai ya hau hanya. Yau ba ya Kaduna, gobe Sakkwato, jibi Zamfara, gata Katsina; kullum yana yi wa gida gibi, cikin abin da ya kamata ya tattala masu.
Gaskiyar Magana, ko aiki ka kawo wa Ado, in yana da wata tafiya gabansa yana neman kudi, zai maza-maza ya yi maka, don ya fitar da ribarsa, ya samu abin karawa gaba. In kuma yasan akwai lokaci, zai ce kawo kafin alkalami. Da wannan abin da ya amsa zai tafi, in ya dawo ka karasa kudin, a yi maka aikin da su. Wani lokaci kuma aikinka na iya makalewa saboda yawan fadi-tashi irin nasa. Ina da ayyuka biyu a hannunsa da suka sargafe. Dayake na san halin ’yan mazan, ban damu ba balle ma dama ban ba da dashen fartanya ba.
Mutum ne wanda ya san mutumcin mai ganin girmansa, yana kuma lankwasuwa; don kana iya canza shi bisa hujja. In ya so kuma dan tasha ne, don ya iya hauragiya, ya kuma iya ya jagoranci a yi tawaye ko ya assasa tawayen.
Bana jin Ado zai iya fadin yawan lambobin yabon da aka ba shi a kan rubutu. A wani lissafi da muka yi da shi fiye da shekaru shida da suka wuce, lokacin da na zo Kano kan littafin Bashir Tofa. A lokacin lissafin na da yawa, har ina yi masa wasa ina cewa ya gina masu dakinsu daban.
Hakika duk wanda ya san Ado da kishinsa a kan adabin Hausa da fadi-tashin da yake, yada shi da kare shi da kudinsa da lokacinsa da karfinsa, ya san ya cancanci wannan lamba. Na taka ’yar rawa har fage biyu wajen Ado ya samu wannan lamba, wanda zan fadi daya yanzu saboda tarihi; dayar kuma zan bar ta. Amma kafin nan, mu uku kadai muka sani. Rawar farko ita ce, wanda ya ba da sunan Ado don a ba shi wannan lamba, ya yi ne bisa kauna da kuma jinjina wa aikinsa; shi ne Sani Mafara.
Sani Mafara, ina daga cikin wadanda yake girmamawa sosai saboda dalilan da shi ya san su amma daga cikinsu, mun dade muna mutunci, yana dauka ta wani yayansa. Kusan wasu abubuwansa bai yin su sai ya tuntube ni shawara.
Mafara dan jarida ne kuma marubuci, yanzu kuma yana aiki Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya. Ya kuma san duk hanyar da ake bi wajen samun lambobin yabo irin wannan. Duk shekara yakan zabi wasu ya sa sunansu kuma a yi bincike a kansu, a tabbatar, a kuma ba su.
Shi ya shaida mani zai zabi Ado na kuma ba shi karfin gwaiwa. Wannan karfafa shi da na yi, ya kara masa azama amma na fada wa Sani Mafara cewa kar ya yi zancen da kowa, kar ya tattauna zaben Ado yake neman yi da duk wani marubuci.
Hikimar a nan, kar ya hadu da wanda zai raunana kudurinsa, don haka ya yi mani biyayya, ya bar abin a zuciyarsa, ya kuma rika bin takardun zaben Ado da ya yi. Mafara kan kawo min ziyara Katsina in ya samu lokaci, duk lokacin da ya zo nakan karfafa shi.
Na shaida masa cewa ya cancanta kuma alfahari ne ga adabin Hausa. Ana sauran kwana 10 a sanar, Sani Mafara yana wajena a Katsina. Ya ce min ai zancen lambar yabo ta Ado, in sha Allah sanarwa kadai ta rage. Na ce ka yi shiru da bakinka. Nan ne Sani ya buga kafa ya ce ai aikin gama ya gama, Allah ne kadai mai canza lamarin nan. Ya ce Shugaban kasa ya sa hannu, ta kuma fito daga ofishinsa. Na kara jaddada masa cewa ka yi shiru a bayyana.
Ana gobe za a bayyana, ya ce man gobe za a saki sunayen nan. Na sake jan hankalinsa ya ja bakinsa ya tsuke. Na so a ce ni ne na farko da na shaida wa Ado cewa yana ciki amma hidima ta dauke min hankali. Sai na tuna cewa yau za a saki sunan, na kira Sani ya tabbatar min cewa an saki sunayen, har da na Ado. Na kira lambar Ado na kuma yi masa tes. Daga baya ya fada min cewa ni ne na biyu da na shaida masa.
Hakika wannan lambar abin alfahari ce ga Adabin Kasuwar Kano. Da fatan sabbin marubuta masu aiki ba tsari za su dau darasi daga yadda Ado ya rika canzawa, yana daidaita sahunsa, ya gyaru.
Wanda kowa ya dauko littafinsa na farko da na baya baya, ya san an taba yin tsohon Ado Ahmad Gidan Dabino, yanzu kuma an yi sabon Ado Ahmad dan shekara 50 da lambar yabo ta kasa, MON