Ado da Bala
Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Ado da Bala, labarin ya kunshi yadda ba a cin riba a mugunta. A sha karatu lafiya. Ado mutum ne mai tausayi da tsoron Allah. Yana da Yaya Bala mai son cin zali da ha’inci. […]
Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Ado da Bala, labarin ya kunshi yadda ba a cin riba a mugunta. A sha karatu lafiya.
Ado mutum ne mai tausayi da tsoron Allah. Yana da Yaya Bala mai son cin zali da ha’inci.
Ran nan Ado ya je rafi sai ya ci karo da wani yaro yana kuka saboda ya rasa hanyar komawa gida. Sai ya ba shi abinci ya ce zai kai shi gida. Nan yaron ya bace ya koma fatalwa. Ya ce zai taimaka masa kamar yadda shi ma ya taimaka masa. Ya ba shi kudi da dama da wata sanda.
A kan hanyar Ado ta komawa gida sai ya ci karo da barayi suka kwace masa kudin.
Yana hurar sandar sai barci ya kwashe barayin, ya kwashi kudinsa ya koma gida sannan ya ba Bala labari.
Bala na jin labarin sai ya yanke shawarar kai ziyara bakin rafi. Sai ya ga wata tsohuwa ta bukaci ya taimaka mata amma ya ki. Ya ce tab! Shi yaro kawai zai taimaka mawa. Haka ya gama zagaye ba tare da ya ga yaron ba, sannan ya koma gida cikin bakin ciki.
Bayan ya koma gida, sai ya lallaba ya sace sandar Ado inda ya nufi gidan Sarki don ya yi sata. Yana isa sai ya hura sandar a zatonsa Sarki da fadawansa za su yi barci, kuma babu mai ganinsa.
Ya shiga fadar Sarki ya rika jidar dukiya. Abin sai ya ba dogarai da Sarki mamaki, alhali suna kallonsa yana sata. Bayan Bala ya gama satar a hanyarsa ta fita ne dograi suka yi kama shi. Bayan sun yi masa dukan tsiya suka aika shi zuwa kurkuku, inda a nan ne ya yi nadamar abin da ya aikata.
Da fatan Manyan Gobe sun dauki darasi daga wannan labari.
Sai mako na gaba insha Allah.