AFAN ta fara raba wa manoma 5,040 takin zamani kyauta a Gombe
Tallafin zai rage wa manoma tsadar noma tare da taimaka musu wajen ƙara yawan amfanin gona a daminar bana.
Ƙungiyar Manoman Najeriya (AFAN) ta fara rabon takin zamani kyauta ga manoma 5,040 a Jihar Gombe, a ƙarƙashin shirin tallafin Asusun Bunƙasa Noma na Ƙasa National Agricultural Development Fund (NADF).
An ƙaddamar da shirin ne bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hannun Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci, da nufin ƙara yawan amfanin gona da tallafa wa manoma a daminar bana.
- Obi ya amince zai yi wa’adi ɗaya idan aka zaɓe shi — Kwankwaso
- Ambaliya ta yi ajalin yara biyu ’yan gida ɗaya suna dawowa daga Islamiyya a Katsina
Da yake ƙaddamar da shirin, Shugaban AFAN na ƙasa, Alhaji Muhammad Magaji Gettado, ya ce kowane manomi da ya ci gajiyar shirin zai karɓi buhunan taki huɗu.
Ya bayyana cewa shirin ya shafi jihohi 25 da Babban Birnin Tarayya (FCT), inda za a raba takin ga dubban manoma.
A cewarsa, AFAN ce ta zaɓi manoma 3,040 a kowace jiha, yayin da gwamnatocin jihohi ta hannun ma’aikatun noma suka ƙara wasu manoma 2,000, wanda hakan ya kai adadin masu cin gajiyar shirin zuwa mutum 5,040 a kowace jiha.
Ya ƙara da cewa an kammala zaɓen sunayen manoman tun a watan Maris da Afrilu, kafin Hukumar NADF ta tantance tare da amince da jerin sunayen.
Gettado ya ce isar da taki ga manoma a kan lokaci na da matuƙar muhimmanci domin samun amfanin gona mai yawa.
“Bayar da taki a kan lokaci yana da muhimmanci kamar samar da takin kansa. Idan manoma sun samu taki a lokacin da ya dace, hakan zai inganta ci gaban amfanin gona da kuma ƙara yawan girbi,” in ji shi.
Shi ma Shugaban AFAN na Jihar Gombe, Ahmed Modibbo Nafada, ya yaba da ƙoƙarin shugabancin ƙungiyar na ƙasa wajen samar da tallafin.
Ya kuma ƙarfafa gwiwar manoman da suka amfana da su yi amfani da takin yadda ya kamata domin haɓaka amfanin gonakinsu.
A nasa ɓangaren, Daraktan Noma na Ma’aikatar Noma ta Jihar Gombe, Ibrahim Sajo, ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da bai wa harkar noma muhimmanci domin tabbatar da wadatar abinci.
Ya ce Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya sayo manyan motocin taki guda 335 domin sayar wa manoma a farashi mai rahusa a faɗin jihar.
A madadin waɗanda suka amfana da shirin, Shugaban Manoman Alkama na Jihar Gombe, Lawan Bala Garba, ya gode wa AFAN da Hukumar NADF bisa samar da takin kyauta.
Ya ce tallafin zai rage wa manoma tsadar noma tare da taimaka musu wajen ƙara yawan amfanin gona a daminar bana.
