AFCON 2019: Dalilan da sauran kasashen Afirka suka cin mana – Dambatta
Babban Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), Farfesa Umar Garba Dambatta ya ce matukar Najeriya ba ta koma ta kintsa ba, kasashe irin su Madagaska za su ci gaba da cimma kungiyar kwallon kafa ta kasa. Da yake karbar bakuncin Darakta Janar na Gidan Talabijin na Kasa (NTA), Alhaji Yakubu Ibn Mohammed, Farfesa Dambatta ya […]
Babban Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), Farfesa Umar Garba Dambatta ya ce matukar Najeriya ba ta koma ta kintsa ba, kasashe irin su Madagaska za su ci gaba da cimma kungiyar kwallon kafa ta kasa.
Da yake karbar bakuncin Darakta Janar na Gidan Talabijin na Kasa (NTA), Alhaji Yakubu Ibn Mohammed, Farfesa Dambatta ya ce a shekarun 1990, Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka yi fice a harkar kwallon kafa inda ake daidaita ta da kasashen Birazil da Ajentina.
“Kowa a yanzu yana maganar kasar Madagaska. Mutane na duba taswirar kasashe don nemo inda kasar Madagaska take amma tasirin da suka yi ya samo asali ne na komawa asali da shirin da suka yi wa gasar. A yanzu kasar na cin moriyar nasarar da ta samu. Amma ka tuna mun samu kanmu a wannan matsayi a baya a kai -a -kai. Kwatsam kawai sai wasu kasashe suka maye gurbin don kuma suna samun nasara cikin sauri. Ya zama wajibi a yi wani abu don kare matsayinmu,” inji shi.
Farfesa Dambatta ya yi kira ga kamfanonin kasar nan su rika tallafa wa harkokin wasanni inda ya ce Hukumar NCC ita ce kan gaba wajen tallafa wa bangaren ta hanyar tallafa wa gasar kwallon Tenis a kasa baki daya.
Sannan Babban Shugaban Hukumar NCC din ya bukaci kamfanoni su hada gwiwa don tabbatar da ganin Gidan Talabijin na NTA ya iya nuna gasar da ke gudana ga ’yan Najeriya kai-tsaye.
Ya bayyana cewa saboda ci gaban kimiyya za a iya kallon wasannin kai-tsaye ta hanyar fasahar sadarwar zamani, inda ya kara da cewa Hukumar NCC tana da nauyin samar da dama da kuma sanya ido kan ingancin harkokin.
Da yake jawabi tun farko, Malam Yakubu Ibn Muhammad wanda ya bayyana wasanni a matsayin kafafe da suke hada kan kasa, ya ce ya ziyarci hedikwatar Hukumar NCC ce don neman goyon baya kan samun yadda za nuna gasar kai-tsaye ga ’yan Najeriya.