AFCON 2019: Gobe Najeriya za ta kece-raini da Kamaru
A gobe Asabar idan Allah Ya kai mu Kungiyar Kwallon Kafa ta Super Eagles ta Najeriya za ta kece-raini da takwararta ta Indomitable Lions da ke Kamaru a wasa zagaye na biyu. Najeriya dai ta gama a matsayi na biyu ne a Rukunin B, yayin da Kamaru ta gama a matsayi na biyu a Rukunin […]
Tambarin AFCON
A gobe Asabar idan Allah Ya kai mu Kungiyar Kwallon Kafa ta Super Eagles ta Najeriya za ta kece-raini da takwararta ta Indomitable Lions da ke Kamaru a wasa zagaye na biyu.
Najeriya dai ta gama a matsayi na biyu ne a Rukunin B, yayin da Kamaru ta gama a matsayi na biyu a Rukunin F, inda hakan ya sa za su hadu a wannan zagaye.
Kamar yadda jadawalin gasar ya nuna, kungiyoyin biyu za su kece-raini ne da misalin karfe 5:00 na yamma agogon Najeriya yayin da mai masaukin baki Masar za ta kece-raini da Afirka ta Kudu da misalin karfe 8:00 na dare duk a goben.
Kodayake Najeriya ce ta doke Kamaru a lokacin da ake buga gasar neman zuwa gasar cin Kofin Duniya da aka yi a Rasha a bara, amma tarihi ya nuna Kamaru ce ta fi doke Najeriya a yawan wasannin da suka hadu a baya.
Kamaru ta samu nasara a wasanni uku daban-daban a kan Najeriya a gasar cin Kofin Afirka a baya don haka wannan shi ne karo na hudu da za su hadu a gasar.
Kamaru ce mai rike da wannan kofi a halin yanzu bayan ta lallasa Masar a wasan karshe da ci 2-1 a shekarar 2017 kuma tarihi ya nuna ta dauki kofin har sau biyar yayin da Najeriya ta dauka sau uku.
Masoya kwallon kafa sun zuba ido su ga yadda wannan wasa zai kaya.