AFCON 2021: Karon battar abokai tsakanin Salah da Mane a wasan karshe
Za a raba gari tsakanin abokai biyu da ke taka leda a kungiya daya, Sadio Mane na Senegal da Mohammed Salah na Masar
Ranar Lahadi, 6 ga Fabrairu, 2022, ne za a rabe aya da tsakuwa a wasan karshe na Gasar Cin Kofin Afirka tsakanin kasar Masar da Senegal a filin wasa na Paul Biya da ke birnin Doula a kasar Kamaru.
Masu kwallo suna ganin wasan a matsayin wanda za a raba gari tsakanin abokai guda biyu da kusan kullum suke tare a kungiya daya suke taka leda, wato Sadio Mane na Senegal da Mohammed Salah na Masar.
- AFCON2021: Senegal da Masar za su kara a wasan karshe
- Zama matar Adam Zango ya jawo min koma-baya –Amina Rani
Tawagar Lions of Teranga ta Senegal ba ta taba lashe gasar ba a tarihinta kuma wannan ne karo na biyu da ta kai wasan karshe a jere.
Kasar Aljeriya ce ta doke Senegal din a wasan karshe na gasar a shekar 2019.
Senegal ta nuna bajinta matuka a wasanninta na zagaye na biyu a gasar, inda a wasa uku na zagaye na biyu din ta zura kwallo 8, ita kuma aka zura mata biyu kacal.
Ita kuwa Masar, ta lashe Gasar Cin Kofin Afirka sau bakwai, sannan wannan ne karo na biyar da za ta buga wasan karshe a gasar shida da ta buga na karshe da suka gabata.
Sai dai kuma za a iya cewa da kyar ta tsallake a duka wasannin guda uku, domin duk sai da aka kai ga buga karin lokaci suke samun nasara. Biyu daga ciki ma da bugun fanarati ne suka tsallake.
Senegal da Masar a tarihi
A tarihi an buga wasa 12 a tsakanin Senegal da Masar, inda Masar ta samu nasara a wasa shida, Senegal ta samu nasara a hudu, sannan aka yi kunnen doki a wasa biyu.
Hasashen ’yan wasan da za su fara:
Senegal
Senegal ba da wata matsala kawo yanzu; Babu dan wasanta da ya sa samu rauni kuma babu wanda aka dakatar.
Da wannan Aminiya take hasashen Senegal za ta zuba zaratan ’yan wasanta:
Edouard Mendy, Bouna Sarr, Kalidou Koulibaly, Abdou Diallo, Saliou Ciss; Cheikhou Kouyate, Nempalys Mendy; Bamba Dieng, Idrissa Gueye, Sadio Mane da kuma Famara Diedhiou.
Masar
A bangaren Masar kuma, asalin golan kasar ya samu sauki ya dawo bayan kokarin da gola na uku Gabaski ya yi har suka kawo wannan mataki na wasan karshe.
Wannan ya sa Aminiya hasashen gola Mohammed Sobhi zai dawo, sai a zuba sauran:
Masar Mohamed Sobhi, Omar Kamal, Ahmed Hegazy, Mohamed Abdelmonem, Ahmed Fatouh; Ayman Ashraf, Mohamed Elneny, Amr El Solia; Mohamed Salah, Mostafa Mohamed, da kuma Trezeguet.
Karon battar Salah da Mane
Anjima kadan za a raba tsakanin Mohammed Salah dan kasar Masar da Sadio Mane dan kasar Senegal a wasan karshen.
Mohammed Salah da Mane abokai ne da suke kwallo tare a kungiyar Liverpool ta Ingila, inda suke matukar jan zarensu tare.
Sai dai kuma a cikinsu babu wanda ya taba lashe Gasar Cin Kofin Afirka.
Sadio Mane ya buga wasan karshe na gasar a wancan karon, inda Aljeriya ta doke su.
Shi ma Salah ya kusa lashe gasar a shekarar 2017 inda kasar Kamaru ta doke su a gasar da ta wakana a kasar Gabon.
Sadio Mane ya zura kwallo uku a gasar ta bana, shi kuma Mohammad Salah ya zura biyu.