AFCON 2023: Ghana ta kori koci da ’yan tawagar horas da ’yan wasanta bayan cire su

Karo na biyu a jere ke nan da tawagar Black Stars ta Ghana take kasa tsallake zagayen farko a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka

AFCON 2023: Ghana ta kori koci da ’yan tawagar horas da ’yan wasanta bayan cire su

Ghana ta sallami mai horas da  ’yan wasanta, Chris Hughton, nan take bayan an lallasa su an koro su gida a zagaye farko na Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON) da ke gudana a kasar Ivory Coast.

Kazalika gwamnatin Ghana ta rusa kwamitin horas da ’yan wasan bayan tawagar ta kasa tsallakawa zuwa zagayen ’yan 16 a gasar.

Hukumar kwallon kafar kasar ta sanar da haka ne a shafinta na intanet, tana mai cewa za ta sabunta dabaru da kuma takun tawagar ’yan wasanta.

Karo na biyu a jere ke nan da Ghana ke kasa tsallaka zagayen farko a gasar AFCON.

A wanna karon Ghana za ta koma gida ne sakamakon yin canjaras sau biyu da kuma rashin nasara daya a matakin rukuni.

Black Stars ta Ghana ta sha kashi da ci 2-1 a hannun kasar Cape Verde, sannan ta yi canjaras da ci 2-2 da kasashen Masar da Mozambique.

Sanarwar da hukumar kwallon kafar kasa ta fitar ta ce, “Hukumar Kwallon Kafa ta Kasar Ghana na sanar da al’umma cewa ta sallami Chris Hughton a matsayin mai mai horas da ’yan wasanta nan take.

“Haka kuma hukumar ta rushe tawagar masu horas da ’yan wasan kungiyar ta Black Stars.

“Nan gaba hukumar za ta sanar da sabbin sauye-sauye da kuma alkiblar kungiyar Black Stars,” in ji sanarwar.

A shekarar 2022 ne Hughton ya fara aiki da Black Stars a matsayin daraktan horaswa, kafin a daga likafarsa zuwa matsayin kociya a 2023.