AFCON 2023: Najeriya tsallaka zagaye na biyu
Kwallaon da Opa Sangante ya ci kasansu ya zame wa Guinea-Bissau karar kwana a gasar da ke gudana a kasar Ivory Coast.
Kungiyar Super Eagles ta Najeriya ta kai kanta zagaye na biyu a Gasar Cin Kofin Afirka da ke gudana bayan ta lallasa Guinea Bissau da ci daya mai ban haushi.
Najeriya ta tsinci dami a kala bayan dan wasan Guineas Bissau, Opa Sangante, ya ci kansu a minti na 37, a kokarinsa na ba da fasin a cikin yadi shida, amma sai kwallon ta wuce mai tsaron ragarsu, ta zama ci.
Kwallaon da Opa Sangante ya ci kasansu ya zame wa Guinea-Bissau karar kwana a gasar da ke gudana a kasar Ivory Coast.
Da nasarar da Najeriya ta samu a fafatawar a aka yi a Filin Wasa na Félix-Houphouët-Boigny, ta samu da maki bakwai da muka matsayi na biyu a rukunin A, wanda kasar Equatorial ke saman teburin rukunin da maki bakwai.
- An haramta hawa babur a Jalingo
- ’Yan majalisar Filato da kotu ta kwace kujerunsu sun lashi takobin dowawa bakin aiki
Kowanne daga cikin kasahen biyu ya samu nasara a wasanni biyu, sannan ya yi canjaras a wasa daya a matakin rukuni.
Mai masaukin baki, Ivory Coast, ta sha da kyar da maki uku, inda ta samu nasara a wasa daya, ta yi rashin nasara a wasanni biyu.
Kasar da ke kasan teburin ita ce Guinea Bissau, wadda za ta koma gida kuma ba ta da maki ko daya.