AFCON 2023: Yau za a kece-raini tsakanin Najeriya da Cote d’Ivoire

A wasannin biyar na karshe na Super Eagles ba ta samu nasara a ko daya ba, Cote d’Ivoire kuwa, ta ci duka wasanninta

AFCON 2023: Yau za a kece-raini tsakanin Najeriya da Cote d’Ivoire

A yau, Alhamis ne za a fafata wasan kece-raini tsakanin tawagar Super Eagles ta Najeriya da takwararta, Cote d’Ivoire, wadda ita ce mai masaukin baki a wasa na biyu na Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON).

Idan ba a manta ba, Najeriya ta tashi daya da daya a wasanta na farko da kasar Equatorial Guinea, wanda ya sa magoya baya da dama na Najeriya suka nuna rashin jin dadinsu da sakamakon, inda wasu suke nuna yatsa ga ’yan wasan da zargin cewa ba su cika buga wa kasar kwallo da zuciya da dagiya ba kamar yadda suke yi a kungiyoyinsu.

A wannan wasan da za a buga a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan, Super Eagles na neman maki uku ne komai rintsi domin samun kwanciyar hankali, da kuma sanyaya zukatan ’yan Najeriya masu bibiyar wasannin, musamman magoya baya, da ma ’yan kasar masu adawa.

Cote d’Ivoire ta yi nasara a wasanta na farko, wanda hakan ya sa take da saukin zullumi a wasan na yau, sanna idan ta doke Najeriya, ta samu nasara biyu ke nan a jere, wanda hakan ke nufin ta tsallaka zuwa zagaye na biyu a gasar. Amma kuma hakan zai zama babbar barazana ga Najeriya.

Babban kalubalen da ke gaban Super Eagles shi ne za ta buga wasa babba, da kasa babba a wasan tamaula, sannan mai masaukin baki kuma a lokaci mai muhimmanci.

Haka kuma Najeriya ta yi rashin matashin dan wasan tsakiyarta, Alhassan Yusuf, wanda za a iya cewa ya shigo tawagar da kafar dama.

Raunin da matashin ya ji a wasan Najeriya na farko a minti 69 da fara wasa, ya sa ba zai samu buga wasan na biyu ba, wanda hakan ba karamin rashi ba ne.

Akwai bukatar samun matashin dan wasan tsakiya mai kwazo da zai yi kokarin hana ’yan wasan tsakiyan Cote d’Ivoire irin su Fofana da ke kwallo a Al Nassr ta Saudiyya da tsohon dan wasan Barcelona da AC Milan, wanda yanzu shi ma yake Al Ahli na Saudiyya, Frank Kessie.

Wasanni biyar na karshe na kasashen biyu

Aminiya ta lura wasannin biyar na karshe na Super Eagles ba ta samu nasara a ko daya baya, inda ta yi 1-1 da Equatorial Guinea a wasan AFCON na farko, sai wanda ke biye masa wanda aka doke Najeriya da ci 2-0 a wasan sada zumunta a Dubai a ranar 8 ga Janairun bana.

Sauran su ne 1-1 da Zimbabwe da irin sakamakon da kasar Lesotho duka a wasan neman shiga Gasar Kofin Duniya sai kuma 2-2 da kasar Saudiyya a wasan sada zumunta.

A bangaren kasar Cote d’Ivoire kuwa, ta ci duka wasanninta guda biyar da suka gabata, inda ta zura kwallo 18, ciki har da lallasa Seychelles da ci 9 da nema.

Hasashen Aminiya kan ’yan wasa 11 da za su fara

Najeriya: Nwabali; Aina, Ekong, Omerou, Zaidu; Onyeka, Aribo, Iwobi; Lookman, Osimhen, Moffi.

Cote d’Ivoire: Fofana; Konan, Ndicka, Diomande, Singo; Sangare, Kessie, Seko Fofana; Bamba, Boga, Krasso.