AFCON 2025: Super Eagles ta tsallaka zagayen ’yan 16
Najeriya ce ke kan ragamar teburin rukunin da maki shida daga wasanni biyu.
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles ta Najeriya, ta tsallaka zagayen ’yan 16, bayan doke ƙasar Tunusiya da ci 3 da 2.
Ƙasashen biyu daga rukunin C, sun ɓarje gumi da misalin ƙarfe 9 agogon Najeriya.
- Ghana ta kama mutum 141 kan zargin aikata damafara a Intanet
- ’Yan ɗaurin aure 7 sun rasu a hatsarin mota a hanyar Borno
Wasan ya ɗauki hankali duba da yadda ƙasashen suka saba haɗuwa a gasar Nahiyar Afirka.
Wasan ya ƙayatar da kallo ganin yadda ƙasashen suka murza leda a daren ranar Asabar a ƙasar Maroko.
Fitaccen ɗan wasan gaban Najeriya da Galatasaray, Victor Osimhen ne, ya fara jefa ƙwallo a ragar Tunusiya a minti na 44.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Kyaftin ɗin Super Eagles, Wilfred Ndidi, ya sake sanya Najeriya a gaba a minti na 50.
A minti na 67 Ademola Lukman ya sake jefa wa Super Eagles ƙwallo ta uku a ragar Tunusiya.
A minti na 74 ne Tunusiya ta yi huɓɓasa ta hanyar jefa ƙwallo ta hannun ɗan wasanta, Talbi.
Shi kuwa Ali Abdi, ya jefa ƙwallonsa a minti na 87 daga bugun fenariti.
Najeriya ce ke jan ragamar teburin rukunin da maki 6 daga wasa biyu da ƙwallo biyar, yayin da aka jefa mata ƙwallo uku a raga.
Ita kuwa Tunusiya tana mataki na biyu a rukunin da maki 3, bayan lashe wasa ɗaya da rashin nasara ɗaya.
Tanzaniya tana mataki na uku, sai Uganda a mataki na ƙarshe, dukkaninsu da maki ɗaya-ɗaya, bayan rashin nasara da yin kunnen doki a wasanni biyu da suka buga.