AFCON: CAF ta bai wa Super Eagles maki, ta ci tarar Libya

CAF ta ci tarar ƙasar Libya Dala 50,000 tare da bai wa Super Eagles maki uku.

AFCON: CAF ta bai wa Super Eagles maki, ta ci tarar Libya

Hukumar Ƙwallon Ƙata ta Afrika (CAF), ta ci tarar ƙasar Libya Dala 50,000 tare da bai wa Super Eagles maki uku, biyo bayan wulaƙanta ’yan wasan Najeriya a ƙasar.

Wannan dai na zuwa ne bayan CAF ta kammala bincikenta tare da samun ƙasar Libya da wulaƙanta tawagar ’yan wasan Super Eagles da gangan.

Idan ba a manta hukumar, ta bayyana cewar za ta gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace.

Dambaruwar da aka samu ne ya sanya Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF), ta kaurace wa wasanta da ƙasar Libya na neman gurbi a Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON) na 2025.

Najeriya ta ta ƙauracewa wasan ne bayan tsare tawagar ’yan wasan na kusan awa 16 a lokacin da suka je wasansu zagaye na biyu a Libya.

Tawagar Najeriya ta dawo gida ne da misalin karfe 5 bayan Gwamnatin Tarayya ta ba su umarnin yin hakan har sai hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta binciki lamarin.

A ranar 1 ga watan Oktoba ne, aka tsara ƙasashen biyu za su fafata bayan wasan farko na neman gurbin shiga AFCON a Najeriya, inda Super Eagles suka yi nasara da ci 1-0.

A yayin da Super Eagles ta je Libya domin buga wasa na biyu ne aka karkata akalar jirginsu zuwa Al Baraq, wanda bayan saukarsu aka hana su fita, suka shafe awa 14 ba tare da abinci ko masauki ba.

Hasali ma, an hana su kama otel domin kwana a yankin bayan saukar jirginsu, gabanin wasan da aka tsara bugawa a birnin Benina.

Haka kuma Kungiyar Kwallon Kafa ta ƙasar Libya ba ta sama musu motocin sufuri ba zuwa inda za a yi wasan a birnin Benina, mai tazarar tafiyar awa biyu.