AFCON: Kudin jirgi zuwa Ivory Coast ya kai N2m
A yau Lahadi ne Super Eagles za ta fafata da Kwaddibuwa, mai masaukin baki
Kudin jirgi daga Najeriya zuwa kasar Kuwaddibuwa ya kai Naira miliyan biyu saboda wasan karshe da tawagar Super Eagles za ta fafata da kasar a Gasar Cin Kofin Afirka.
A yau Lahadi ne Super Eagles za ta fafata da Kwaddibuwa, mai masaukin baki, wadda daga Legas ba ta fi tafiyar sa’a daya da minti 30 a jirgin sama ba.
Sai dai tashin gwauron zabon ya kawo cikas ga ’yan Najeriya da dama da suka yi shirin zuwa kasar domin kallon wasan a birnin Abidjan.
Kamfnonin jiragen saman Najeriya irin Air Peace da Asky da kuma Air Cote d’Ivoire, kadan ne daga cikin masu zirga-zirga zuwa zuwa Abidjan.
- Tsadar Rayuwa: Komawa Ga Allah Shi Ne Mafita —Sarkin Musulmi
- An kama fasto kan safarar yaran Arewa zuwa kudancin Najeriya
Sai dai gabanin wasan na karshe dai an yi ta ce-ce-ku-ce kan tashin kudin jirgi zuwa Abidjan, inda bincike ya nuna tikitin zuwa daga Legas kadai ya kai N890,000 zuwa Naira miliyan 1.2, na zuwa da dawowa kuma ya haura Naira miliyan biyu, ya danganta da kamfanin jirgin sama.
Shafin Asky ya nuna cewa farashin tikitin zuwa kadai ranar Lahadi da za a buga wasan karshen ya kai Naira 1,229,811.
Air Cote d’Ivoire kuwa, farashin jirgin ya kai $913, wanda ya haura N1.3m a kan N1,450 zuwa dala daya.
Wata farfesa a fannin shari’a, Joy Ezeilo (SAN), ta koka kan farashin tikitin, jirgi zuwa Abidjan, inda ta so zuwa kallon wasan AFCON kai tsaye, amma ta kadu da jin farashin tikitin da ya haura N2.1m.
Ta rubuta, “Na so zuwa Abidjan don kallon wasan karashe da za buga da Super Eagles a gasar AFCON 2024 kai tsaye, wanda na zan ba zai tsada ba .
“AMma da na tambayi ejen din dina na sama da shekaru 20, farashin da ya aiko min ya kai N2,183,000.00, wanda ya ba ni mamaki matuka.”
Sai dai ta yi nuni da cewa ta yi wani tsari na daban wanda ya hada da sa katin DSTV sannan ta sayo lita 20 na man fetur domin saboda janaretonta saboda ba su da wutar lantarki domin kallon wasan na karshe.
“Ana ci gaba da gwagwarmaya! Sa’a ga Super Eagles namu! Kuna cikin tunanina da addu’a,” in ji ta.
Sai dai wani mai ba da shawara kan harkokin sufurin jiragen sama, Babatunde Adeniji, ya ce rububin neman tikitin jirgi zuwa Abidjan ne ya haddasa tsadar.