AFCON: Super Eagles sun kaurace wa wasa da Libya
Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) ta kaurace wa wasanta da ƙasar Libya na neman gurbi a Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON) na 2025.
Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) ta kaurace wa wasanta da ƙasar Libya na neman gurbi a Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON) na 2025.
Najeriya ta ta ƙaurace wa wasan ne bayan tsare tawagar ’yan wasan na kusan awa 16 a lokacin da suka je wasansu zagaye na biyu a Libya.
Tawagar Najeriya ta dawo gida ne da misalin karfe 5 bayan Gwamnatin Tarayya ta ba su umarnin yin hakan har sai hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta kammala bincike kan lamarin.
A ranar 1 ga watan Oktoba ƙasashen biyu sun bayan wasan farko na neman gurbin shiga AFCON a Najeriya, inda Super Eagles suka yi nasara da ci 1-0.
A yayin da Super Eagles ta je Libya domin buga wasa na biyu ne aka karkata akalar jirginsu zuwa Al Baraq, onda bayan saukarsu aka hana su fita, suka shafe awa 14 ba tare da abinci ko masauki ba.
Hasali ma, an hana su kama otel domin kwana a yankin bayan saukar jirginsu ranar Lahadi, gabanin wasan da aka tsara bugawa a birnin Benina.
Haka kuma Kungiyar Kwallon Kafa ta ƙasar Libya ba ta sama musu motocin sufuri ba zuwa inda za a yi wasan a birnin Benina, mai tazarar tafiyar awa biyu.