AFCON: Yau za a kece raini tsakanin Najeriya da Sudan

Idan Najeriya ta doke Sudan a yau, za ta iya tsallake kai-tsaye zuwa zagaye na biyu na gasar.

AFCON: Yau za a kece raini tsakanin Najeriya da Sudan

‘Yan wasan Najeriya suna motsa jiki

A Yau Asabar ce za a fafata tsakanin Super Eagles ta Najeriya da Sudan Falcons ta Sudan a wasa na biyu na Gasar Cin Kofin Afirka.

A rukunin D, Najeriya ce ta daya a yanzu haka bayan ta doke Masar da ci daya mai ban haushi, sannan Sudan da Guinea-Bissau suka yi kunnen doki.

Idan Najeriya ta doke Sudan a yau, za ta iya tsallake kai-tsaye zuwa zagaye na biyu na gasar ke nan.

Tarihin wasa tsakanin Najeriya da Sudan

A wasa 14 da aka doka tsakanin Najeriya da Sudan tun wasansu na farko a shejarar 1963, Najeriya ta samu nasarar a takwas, Sudan ta samu nasara a biyu, sannan aka yi kunnen doki sau hudu.

Hasashen ‘yan wasa 11 da za su fara wasa da tsarin wasa.

A hasashen Bakin Raga na Aminiya, muna tunanin a ‘yan wasan da suka buga wasa da Masar, mutum daya kawai za a canja, wato Ola Aina, inda za a iya mate gurbinsa da Ebuehi kasancewar ya fi shi kokarin fita ta taimakawa ‘yan wasan gaba.

Ga jerin ’yan wasan Najeriya tare da lambobin da kowannensu ke goyawa, wanda ake hasashen za su fara wasa da Sudan:

1. Maduka Okoye
2. Tyronne Ebuehi
22. Kenneth Omeruo
5. William Troost Ekong, (C)
12. Zaidu Sanusi
4. Wilfred Ndidi
10. Joseph Aribo
17. Samuel Chukwueze
15. Moses Simon
14. Kelechi Iheanacho
19. Taiwo Awoniyi,

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara