Afghanista ta fara tattunawar sirri da ’yan Taleban
Shugaba Hamid Karzai na kasar Afghanistan ya fara tattaunawar sirri da shugabannin kungiyar ’yan Taleban, ta yadda za a shawo kansu su kulla yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatinsa, kamar yadda jaridar New York Times ta ruwaito, inda ta ce ta jiwo daga wata majiya a Afghanistan da kuma jami’an nahiyar Turai wadanda ba su so […]
Shugaba Hamid Karzai na kasar Afghanistan ya fara tattaunawar sirri da shugabannin kungiyar ’yan Taleban, ta yadda za a shawo kansu su kulla yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatinsa, kamar yadda jaridar New York Times ta ruwaito, inda ta ce ta jiwo daga wata majiya a Afghanistan da kuma jami’an nahiyar Turai wadanda ba su so a bayyana sunansu.
Mai magana da yawun Shugaba Karzai ya tabbatar da cewa an fara tuntubar ’yan Taleban, kuma ya yi nuni da cewa a watnni biyu asuka wuce ana ganin alamun nasara.
Sai dai jami’an hukuma da jaridar ta tuntuba, sun bayyana cewa tattaunawar da aka fara da ’yan Taleban ba ta yi wani alfanu ba a halin yanzu, duk da cewa sun yi nuni da adawar Mista Karzai a kan Gwmanatin Washington.
A watan Nuwambar bara, lokacin da aka fara tattaunawar sirri, Mista Karzai ya nuna kin amincewarsa ta sanya hannu kan yarjejniyar tsario tsakanin gwamnatinsa da Amurka, har sai an kammala zaben shugaban kasa a Afrilun bana. Kuma ya bayyana aniyarsa ta sakion wasu daruruwan fursunonin Taleban da ba a same su da laifi ba. Shugaban dai ya shafe wa’adin mulkinsa sau biyu, don haka ba zai sake tsayawa takara ba.