Afghanistan ta gudanar da zabe lafiya
A ranar Asabar da ta gabata ne jama’ar kasar Afghanistan suka je rumfunan zabe don kada kuri’ar zaben sabon shugaban da zai maye gurbin Shugaba Hamid Karzai.Gabanin zaben dai, kungiyar Taliban ta sha alwashin kaddamar da hare-hare fiye da 1000, a fatan ta na hana jama’ar kasar fitowa rumfunan zabe don jefa kuri’a. Amma ba’a […]
A ranar Asabar da ta gabata ne jama’ar kasar Afghanistan suka je rumfunan zabe don kada kuri’ar zaben sabon shugaban da zai maye gurbin Shugaba Hamid Karzai.
Gabanin zaben dai, kungiyar Taliban ta sha alwashin kaddamar da hare-hare fiye da 1000, a fatan ta na hana jama’ar kasar fitowa rumfunan zabe don jefa kuri’a. Amma ba’a fuskanci wani gagarumin hari ba a lokacin gudanar da zaban kuma ba yadda kungiyar ta so ba, jama’ar kasar sun fito kwanso da kwarkwata wanda hakan ke nuna yadda zaman lafiya ke kara wanzuwa a cikin kasar a dai-dai lokacin da dakarun kasashen waje ke gab da ficewa daga kasar.
Ana ci gaba da kidaya kuri’un da aka kada inda ‘yan takara takwas suka fafata. Akwai dai alamun cewa zaben zai kai har zuwa zagaye na biyu amma zuwa yanzu ‘yan takara biyu ne ke kan gaba wato Abdullah Abdullah na jam’iyyar National Coalition, sai kuma Ashraf Ghani wanda yake takara ba a karkashin kowace jam’iyya siyasa ba. Wannan ne dai karo na farko da wata gwamnatin farar hula za ta mika mulki ga wata a kasar.