Afirka ta Kudu idan maye ya manta…

Kasar Afirka ta Kudu na cikin kasashen da Turawan mamaya na mulkin mallaka na Birtaniya suka yi ma mulkin mallaka. Lokaci mai tsawo kafin mulkin mallaka, Turawa sun shigo kasar Afirka ta Kudu, da sauran yankunan Kudancin Nahiyar Afrika suka mamaye su, suka raba su da gonakinsu, suka mayar da su leburori, ’yan baraima. Bayan […]

Afirka ta Kudu idan maye ya manta…

Kasar Afirka ta Kudu na cikin kasashen da Turawan mamaya na mulkin mallaka na Birtaniya suka yi ma mulkin mallaka. Lokaci mai tsawo kafin mulkin mallaka, Turawa sun shigo kasar Afirka ta Kudu, da sauran yankunan Kudancin Nahiyar Afrika suka mamaye su, suka raba su da gonakinsu, suka mayar da su leburori, ’yan baraima. Bayan Turawa sun kwace kasar daga hannun bakake, sun maida su bayi kaskantattu, sun zo sun shimfida mummunan mulkin wariyar launin fata wanda babu mai muninsa a duniya.

Bakaken fatar Afirka ta Kudu sun sha azaba a hannun Turawan mulkin wariyar launin fata. Sun rasa gonakinsu, sun rasa ’yancinsu na mulkar kai, sannan sun rasa daidaito a wuraren ayyukansu. Ga azabtarwa ga garkamewa.

A lokacin da ake cikin azabtar da bakaken fatar Afirka ta Kudu, dukkan kasashen Afirka da ma duk inda bakar fata yake, an hada kai, aka yaki mulkin wariyar launin fata. An yi amfani da Kungiyar Hada kan Kasashen Afirka (OAU) da Majalisar Dinkin Duniya (UN), an yi amfani da kungiyoyin ma’aikata da kungiyoyin kwadago da na malaman jami’a da dalibai da sauransu, wajen yakar mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu. Daga Najeriya zuwa Aljeriya da Jamaika zuwa bakaken fatar Amurka, an hada kai aka yi ta fafutika don ganin bakaken Afirka ta Kudu sun samu ’yancinsu. A wancan lokaci Allah kadai Ya san makudan kudade da duniya ta kashe wajen yakar mulkin wariya na Afirka ta Kudu.

An shirya daruruwan tarurruka, wasu a makarantu, wasu a dakunan taro, an shirya jerin gwano daruruwa, an buga littatafai, an buga mujallu, an buga kasidu, an rera wakokin kin mulkin wariyar launin fata, an yi abubuwa ba iyaka, mutane da yawa sun rasa rayukansu, saboda bakaken fatar Afirka ta Kudu su rayu. Amma kash, sakayyar da mutanen Afirka ta Kudu ke yi wa sauran kasashen Afirka bakaken fata, ita ce kisansu da kone musu dukiya da korar kare da suke yi musu. Abin takaici, shi ne, yadda jami’an gwamnatin Afirka ta Kudu suke kara nuna goyon baya ga wannan ta’addancin na ’yan kasarsu, inda gwamnatin kasar ke daukar matakai masu tafiyar hawainiya game da kawo karshen rawan daji ake yi kan baki bakake da muke gani a Afirka ta Kudu.

Hausawa na cewa rama cuta ga macuci ibada ce, amma a ra’ayina, bai kamata kasashen Afirka su maida raddi ta hanyar lalata dukiya da rayukan ’yan kasar Afirka ta Kudu ba; sai dai ya kamata a hukunta shugabannin Afirka ta Kudu wadanda ke nuna goyon bayan kyamar baki. Ya kamata kasashen Afirka su hada kai, su yi magana da murya daya, kuma su dauki mataki kwakkwara na hukunta kasar Afirka ta Kudu, domin idan suka ki yin haka, to hadin kan Afirka da magabanta suka sadaukar da rayukansu wajen assasa shi zai raunana. Matakin da Shugaban Kasar, Cyril Ramophosa ya dauka na tura, wasu jakadai su bada hakuri, bai wadatar ba, tunda har yanzu ana ci gaba da maido ’yan kasashen waje da ke zaune a kasar Afirka ta Kudu zuwa kasashensu na asali. Mataki ne na ihu bayan hari wanda ba zai kawo karshen kyamar baki a kasar ba. Kyamar baki ba ta da bambanci da wariyar launin fata ko mulkin wariya da kasar ta yi a baya.

Baya ga hukunta Afirka ta Kudu, ya kamata shugabannin Afirka su maida hankali kwarai da gaske wajen sake hada kawunan mutanen Afirka. Ga dukkan alamu da yawa mutane ba su san inda aka fito ba. Kuma yau za ka ga dan Nijar yana jin haushi dan Najeriya, dan Najeriya na jin haushin dan Kamaru, duk ire-iren wadannan ne ke iya rikidewa su haifar da kyamar baki. Dubi abin da ke faruwa a kasar Libya, duk wannan na nuna yadda al’amura ke kara tabarbarewa a Afirka ne.

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa Masu Rajin Hadin kan Najeriya (08165270879)