Afirka ta Kudu na bukatar canjin shugabanci kamar Zimbabwe – Jigon Jam’iyyar ANC

Wani jigo a Jam’iyyar ANC mai mulki a kasar Afrika ta Kudu ya ce kasar na bukatar canjin shugaban kamar kasar Zimbabwe, inda ya ce ya kamata Jam’iyyar ta yi amfani da taronta na wata mai zuwa domin tsige Jacob Zouma.  Jam’iyyar ta ANC mai mulki ta shiga cikin rigingimu, inda har ta barke gida […]

Afirka ta Kudu na bukatar canjin shugabanci kamar Zimbabwe – Jigon Jam’iyyar ANC

Wani jigo a Jam’iyyar ANC mai mulki a kasar Afrika ta Kudu ya ce kasar na bukatar canjin shugaban kamar kasar Zimbabwe, inda ya ce ya kamata Jam’iyyar ta yi amfani da taronta na wata mai zuwa domin tsige Jacob Zouma. 

Jam’iyyar ta ANC mai mulki ta shiga cikin rigingimu, inda har ta barke gida biyu. Yayin da wasu ke goyon bayan Nkosazana Dlamini-Zouma, wadda tsohuwar matar shugaban kasar ce, kuma ta taba rike minsita a kasar, wasu kuma suna goyon bayan mataimakin Shugaban kasar na yanzu Cyril Ramaphosa.

Jigon jam’iyyar, Jackson Mathembu, wanda kuma shi ne mai ladabtarwar jam’iyyar ya shaida wa kafar Reuters cewa duk wanda jam’iyyar ta zaba ya zama shugaban jam’iyyar a wata mai zuwa, ya zama dole a gare shi ya kawar da Shugaba Jacob Zouma domin jam’iyyar ta gyara lamuranta.

“Ba zai yiwu a bar shi ya ci gaba da mulki ba,” inji shi.

Mthembu ya ce ya kamata jam’iyyar ANC ta koyi darasi daga abin da ke faruwa a kasar Zimbabwe, inda jam’iyyar ZANU-PF mai mulki ta jagoranci tursasa Robert  Mugabe yin murabus

Kafar Yahoo dai ta ruwaito cewa Mthembu yana goyon bayan Ramaphosa ne ya zama shugaban jam’iyyar. Sannan ya ce ya kamata jam’iyyar ANC ta dawo da martabarta a idon ‘yan kasar, bayan an samu labarin cewa wasu ‘yan kasuwa na kusa da Zouma suna da ta cewa wajen bada mukamai a kasar, duk da cewa sun karyata zargin.

Shugaba Zouma zai kammala wa’adinsa na biyu ne a karshen shekarar 2019, amma kuma za a iya tursasa shi ya sauka kafin wa’adin ya kare kamar yadda aka yi wa Thabo Mbeki a shekarun baya.

A watan Mayu, Zouma ya sha da kyar a hannun ‘ya’yan jam’iyyar bayan an gabatar da kudurin cewa ya yi murabus, sannan kuma a watan Agusta ya tsallake rijiya ta baya daga wajen ‘yan majalisa bayan majalisar kasar ta tayar mai da hankali.

Har yanzu Jacob Zouma na da mutane a jam’iyyar, wadanda suka hada da mata, wadanda suke da yawa da kuma karfi a jam’iyyar, da kuma matasan jam’iyyar.