Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga Amurka

Matakin da Amurka ta ɗauka na korar jakadan Afirka ta Kudu, Ebrahim Rasool, abin takaici ne.

Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga Amurka

A ranar Juma’a ce Amurka ta bai wa Jakadan Afirka ta Kudu, Ebrahim Rasool, wa’adin sa’o’i 72 ya tattara komatsai ya fice daga ƙasar.

Hakan na ƙunshe cikin wata ’yar taƙaitacciyar sanarwa da mai magana da yawun ma’iakatar harkokin wajen Amurka, Chrispin Phiri ta fitar.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya zargi Ebrahim Rasool da kasancewa “ɗan siyasar wariyar launin fata mai ƙyamar Amurka,” lamarin da ya ƙara rura wutar rikicin diflomasiyya da ya kunno kai tsakanin Washington da Pretoria.

A cikin watan Fabarairun da ya gabata ne Shugaba Donald Trump ya wallafa wani saƙo a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa Amurka ta dakatar da duk wani tallafi da take bai wa Afirka ta Kudu, sakamakon zarginta da ƙwace gonakin fararen fata na ƙasar.

Wannan dalili ne ya sa shugaba Trump ya sanar da cewa duk wani manomi da aka kwace wa gona, kuma yake fatan koma wa Amurka to zai samu izinin zama ɗan ƙasar cikin sauƙi.

Afirka ta Kudu ta yi martani

Matakin da Amurka ta ɗauka na korar jakadan Afirka ta Kudu “abin takaici ne,” kamar yadda ofishin shugaban ƙasar ya bayyana a ranar Asabar, yana mai kira ga “gyara diflomasiyya” tsakanin ƙasashen biyu.

“Fadar shugaban kasa ta lura da abin takaici na korar jakadan Afirka ta Kudu a Amurka, Mista Ebrahim Rasool,” in ji sanarwar da Fadar Shugaban Afirka ta Kudu ta fitar.