Afuwar Haurobiyawa ko ta Baba-Ojo?
Masu bibiyar tsomomuwar Damo-da-kura-da-diyya a kasar Haurobiya sun cika da ta’ajibin ganin yadda Yadda Dumu-dumu Muzu-muzu, Shagaban Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge da Dauda-mai-maki suka rankaya zuwa fadar BabaOjo, inda suka baje warwas suna rokon afuwar Mai gonakin Ottawa. Wasu kuma sun fasko cewa, ana so a dan kara masa wani kaso ne […]
Masu bibiyar tsomomuwar Damo-da-kura-da-diyya a kasar Haurobiya sun cika da ta’ajibin ganin yadda Yadda Dumu-dumu Muzu-muzu, Shagaban Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge da Dauda-mai-maki suka rankaya zuwa fadar BabaOjo, inda suka baje warwas suna rokon afuwar Mai gonakin Ottawa. Wasu kuma sun fasko cewa, ana so a dan kara masa wani kaso ne a Kamfanin jirga Haurobiya, ta yadda za a shawo kansa ya zo a ci gaba da jefa talakawa cikin talalar talauci; a yi ta salwantar da rayuka da asarar dukiya, uwa-uba a raba kan al’umma, ta yadda za a ji dadin tarkata duk wani kayan alatun kyautata walwalar al’umma zuwa Hauren Danja. Watakila ba su taki sa’a ba, domin Baba-ojo, babban gunkinsu furta kalamai masu daci.
Jin wannan tsomomuwa ta shagabannin Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, sai na tabbatr suna da tabin kwanya, tunda afuwar Baba-ojo suke nema ba ta Haurobiyawa ba. Kodayake suna ganin bas u munana wa Haurobiyawa, Shi ya sa ma Shugaba Jatau Mai-sa-in-sa ya turo Asararren Dokinbobo ko in ce “Asara-dan-kwabo,’ da Kansakalin Kuku su yi wa Haurobiya ruywan ashar, har ma da burgar cewa, matukar Baushensu bai koma kan karagar mulki ba, a shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje, to za su fafata yaki da kasar Haurobiya.
Dumu-dumu Muzu-muzu ya roki Baba-ojo mai gonakin Ottawa kan lallai ya dubi girman Mai-duka ya yi musu afuwa. Sannan ya yi ikrarin cewa, sun tafka kwakyariya data’asa, amma tunda su ’yan dugwi-dugwi din akurkinsa ne, ya kamata ya yi musu afuwa. Shi kuwa gogan naku, Mai gomnakin Ottawa, ganin ya samo gangara, sai kawai ya shiga taratsi, yana ta caccakarsu, har ma ya karkare da furta cewa, shi ya daina wasan Samson-siya-siya da dama-dama-da-kurda-kurda a tsarin damo-da-kura-dadiya.saboda haka ya daina kutsa kai cikin gungun masu jirga al’umma.
A matsayina direban allin wannan farfajiya, na tabbatar da cewa mai dan boto da sanda jirge ta jirga kanta, saura kadan ta jirkice, domin sun susuce, tamkar masu wasan “Majigin kanen-Audu,” hart a kai ga sun rasa wane irin majigi za su shirya wa Haurobiyawa, yadda za a jefa kwanyarsu cikin dawurwuri, a yi sabi zarce. Kai al’amarin da kamar wuya, ‘wai gurguwa da auren nesa.”
Haurobiyawa dai sun ce, “tarwada na ganinku masu fatsa da fantsama koma.’ Da gani dai ‘cinnaka allanguburo ne.’ Haurobiyawa sun gaji da yamutsin Harambata Bobo da kwambon Bobo; ga Ciwon-cibin-boko; ga tsomomuwar tsuntsun limamin majami’ar addu’a da gicciye, wanda aka dibge da damin dalar Harun Amurkawa za a arce da su ta Kudancin Ifrikiyya, ind amahukunta suka cafke su.
Ina da tabbacin cewa, duk sa’adda Haurobiyawa suka fasko dimbin ta’asar da mai dan boto ta tafka musu a tsawon shekarun da ta shafe ta wasan damo-da-kura-da-diya, tabbas al’umma za ta bijiro da tambaya kan afuwar Baba ojo ko Haurobiyawa ya kamata a nema?
Ganin cewa, na kwadi ya kare a dan kada, shi yasa duk sa’adda aka koka kan nuna gazawar mulkin jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, sai kawai jiga-jigan jirga al’umma su fake da cewa, wai ’yan adawa ne ke kawo musu cikas. Da yake kwanyarsu ta dusashe, sai sukakakaba wa kansu tagiyar Malam Mantau, alhali Haurobiyawa duk sun kwafa darar Malam Tunau, shi yasa aka cika kundin labaran da, da na yanzu da nau’ukan ta’asar da masu mulkin Haurobiya suka tafka a kwanon tasa, shi yasa ma suke ta sa-in-sa, wajen gudun-loko da yunkurin jona-tantin mulkin mulaka’u.
Ni dai zan karkare darasina a wannan mako da batun da na samu a kan hanyata ta zuwa wannan makaranta da sanyin safiyar Tabawa ranar sa’a. Mai bada labari ya bayyana cewa:
“Wata ’yar dugwi-dugwi din baba da ke koyon yadda ake kwankwadar furar ilimi a mashayar fura-mai-kyau da ke birnin Haurubja, kuma ’yar aji ta tsayuwa bisa kafa daya ta bijiro da ayar tambaya kan ciwon cabin boko da ya ki ci, ya ki cinye, in data ce wa Sani’ata Fallen-keke, ‘wai yaushe za ku kwanto adon-gari, ’yan uwanmu sama da dari karamin lauje da kuka yi garkuwa da su?” Wannan al’amari dai haka aka kare da takaddama, inda Sani-atta Fallen-keke ta yi ta kokarin shawo kan ’yar dugwi-dugwi ta yarda cewa ba su suka sace adon gari ba, amma ta ki yarda.
karshen dai tika-tika-tik! Tazarce ko ta-zame. Mu daina adawar shiga cikin dawa da zarar mun fasko cewa babu dawa. Domin babu yadda za a yimasu zaluntar al’umma su dore. Mu dai mu ci gaba da roko Mai-duka, mu kuma sauya miyagun dabi’unmu da miyagun ayyukan da muke tsuwurwurtawa, ta yadda Mai-duka zai ji kanmu.
Sakon makaranta
Gizago ya rantse, Dodo ya rates. Daga Salisu Magaji.
To ’yan makaranta kun ji yaron can na bayan Kada, wanda ke lalubemn-koko a wayoyin lantarki, ya fara tsokanarmu. Ba wani ba ne illa Mai motar roba. To ku sanar da shi cewa, Dodo ba ya wargi da ’yan dugwi-dugwi. Ni watsattsake da buda wgagen littattafai ni nusar da su yadda ake yi. To ka ji!