Agwagwar teku da ta shekara 70 a raye
An fara gano ta ce a 1956, inda a yanzu haka take da shekara 70
Wani nau’in agwagwar teku da ake kira da Albatross na cikin nau’in tsuntsaye da aka tabbatar sune mafiya tsawon rai a duniya inda daya daga cikinsu ta kai shekara 70 yanzu haka a duniya.
Daya daga cikin agwagin wadda ake kira da Wisdom, masana ilimin halitta sun ce an fara gano ta ce a 1956, inda a yanzu haka take da shekara 70 kuma ta sake kyankyashe wani da a kwanakin baya.
An fara gano agwagwar ce a 1956, inda wani masanin ilimin halittu mai suna Chandler Robbins, ya gano shekar tsuntsuwar a kusa da sansanin sojin ruwa na Amurka a Midway Atoll wanda shi ne mafi girma a duniya da nau’o’in agwagin (albatross) suke taruwa.
Wisdom ta girmi mutumin da ya gano ta kuma dukkan ’yan uwanta maza ne.
Duk da cewa akwai jinsin aku da aka kiwata da suka rayu kusan shekara 100, tsuntsayen daji ba su cika kai wadannan shekaru ba, amma wannan jinsin agwagi idan ba rashin lafiya ba sukan rayu na
sama da shekara 70.
Sukan yin farautar wasu halittu kuma sukan fuskanci karancin abinci, an gano sukan nemi sharar robobi idan sun rasa
abinci, duk da cewa abubuwa ne masu barazana ga rayuwarsu.
Duk da ba kasafai ake ganinsu ba, suna da dabarar rayuwa fiye da kowane tsuntsun da mutum ya sani.
“Kowace shekara Wisdom takan dawo inda take kiwo, muna da masaniya game da tsawon lokacin da tsuntsayen teku za su iya rayuwa da kuma rainon ’ya’yansu,” wani jami’i a Ma’aikatar Kifi da Namun Daji ta Amurka, Beth Flint ya shaida wa
kafar labarai ta NPR.
“Komawarta ba wai kawai ta zaburar da masu son tsuntsaye a ko’ina ba ne, har ma tana taimaka mana wajen fahimtar yadda za mu iya kare wadannan tsuntsayen teku masu kyau da kuma mazaunin da suke bukata don rayuwa a nan gaba,” inji shi.
A cikin shekara 10 da suka gabata, Wisdom ta burge masana kimiyya kan yadda take iya rayuwa yayin da take shawagi na dubban mila-milai don neman abinci da kuma kula da ’ya’yanta.
Wadansu masanan halittu sun yi imanin cewa, agwagin albatross na bullo da wani tsari na musamman da zai ba su damar guje wa dabbobi masu farautarsu kuma hakan ya taka rawa sosai ga tsawon rayuwarsu.
“Ina tsammanin cewa, a shekarun da suka wuce, tabbas Wisdom ta koyi guje wa mafarauta a cikin teku, kuma ta koyi yin kiwo da kyau kuma ta yiwu ta guje wa robobi a kwanakin nan da tasoshin kamun kifi,” inji John Klavitter na Hukumar Midway Atoll National Wildlife Refuge, wanda yake masanin halittu.
Tsuntsuwar na kyankyashe kwai xaya ne kawai a cikin shekaru kadan, kuma Hukumar Kifi da Namun Daji ta Amurka (USFWS) ta yi imanin cewa, jinsin tsuntsuwar kan kyankyashe ’ya’ya 30 zuwa 36 a rayuwarta, wanda shi ne na karshe a farkon wannan shekarar.
Tsuntsun da yake tare da Wisdom shi ne ake wa lakabi da Akeakamai na karshe da ya kasance tare da ita tun 2010.
“Mun yi imanin Wisdom ta samu wasu ’yan uwanta,” inji Dokta Beth Flint.
“Kodayake agwagwar kan samu wasu ma’aurata, za su iya samun sababbin abokan tarayya idan bukatar hakan ta taso.”