Ahmed Lawan ya roki ’yan Najeriya su sake ba APC dama a 2023
Ya ce APC ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da inganta rayuwar ’yan Najeriya
Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmed Lawan, ya roki ’yan Najeriya da su sake ba jam’iyyar APC dama ta ci gaba da mulkin Najeriya a 2023.
Ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da Sanata mai wakiltar mazabar Kwara ta Tsakiya a Majalisar, Sanata Ibrahim Yahaya Oloriegbe ya shirya ranar Asabar.
- ’Yan bola jari sun zargi ma’aikata da kone dukiyarsu ta N70m a Ogun
- Sojojin Isra’ila sun kashe Bafalasdine, sun jikkata wasu mutum 13
A yayin taron dai, wanda ya gudana a Ilorin, babban birnin Jihar ta Kwara, Sanata Oloriegbe, ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar kujerar a karo na biyu.
Tun da farko dai sai da Sanata Ahmed Lawan ya kaddamar da fara aikin gyaran wani asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Budo-Egba a Karamar Hukumar Asa, sannan ya kaddamar da wani asibitin a gundumar Idi-Isin a yankin Okolowo na Ilorin.
Sai dai ya gargadi ’yan Jihar ta Kwara kan sake komawa mulkin PDP a Jihar.
Shugaban Majilisar ya kuma ce ayyukan da Sanata Oloriegbe ya aiwatar a mazabar sun shafe na duk wanda ya taba darewa kujerar kafin shi, cikinsu har da tsohon Shugaban Majalisar, Sanata Bukola Saraki.
“Ina kuma so in yi kira ga ’yan Najeriya da su sake ba jam’iyyar APC dama a 2023. Mun yi wa mutane alkawarin yin bakin kokarinmu, kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba,” inji Ahmed Lawan.
Shi ma da yake nasa jawabin, Sanata Oloriegbe, ya tunatar da mutanen Jihar yadda suka kawo karshen mulkin ’yan gida daya a Jihar da aka yi wa lakabi da ‘O to ge’ a 2019.
Ya ce wakilcin shi a majalisar ya samar wa mutanen mazabarsa alkibla tun 2019, tare da rokon su su sake ba shi dama a zabe mai zuwa.