Ahmed Manir na APC ya lashe zaben kujerar majalisar wakilai na mazabar Lere
Injiniya Ahmed Manir na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben kujerar majalisar wakilai ta tarayya, ta mazabar Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, a zaben da aka gudanar a ranar asabar da ta gabata. Inda ya kayar da Alhaji Muhammad Lawal Rabi’u na jam’iyyar PDP da yake kan wannan kujera. Da take bayyana sakamakon […]
Injiniya Ahmed Manir na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben kujerar majalisar wakilai ta tarayya, ta mazabar Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, a zaben da aka gudanar a ranar asabar da ta gabata. Inda ya kayar da Alhaji Muhammad Lawal Rabi’u na jam’iyyar PDP da yake kan wannan kujera.
Da take bayyana sakamakon zaven a garin Saminaka, a daren ranar lahadin nan, babbar jami’ar Hukumar Zabe ta kasa INEC da ta tattara sakamakon zaben Farfesa Maryam Suleiman ta bayyana cewa Ahmed Manir na Jam’iyyar APC ya sami kuru’u dubu 64, 442. A yayin da Alhaji Muhammed Lawal Rabi’u na jam’iyyar PDP da yake kan wannan kujera ya sami kuru’u dubu 29,706. Don haka ta ce Ahmed Manir na jam’iyyar APC ne ya lashe wannan zabe.
Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan kammala sanar da zaben, Injiniya Ahmed Manir ya bayyana cewa gaskiya yaji dadin irin goyan baya da hadin kan da al’ummar Karamar Hukumar Lere suka bashi.
Ya ce yaji dadin yadda aka yi wannan zabe cikin kwanciyar hankali kuma aka bar jama’a suka zabi abin da suke so.
‘’Babu abin da zan cewa al’ummar Karamar Hukumar Lere sai dai na mika godiyata a gare ku. Kuma da yardar Allah zan rike wannan amana da kuka damka mani’’.
Ya ce dukkan al’ummar wannan karamar hukuma sun ganewa idanunsu irin ayyukan da ya fara tun kafin a zave shi. Don haka ya yi kira a cigaba da yi masa addu’a domin ya cigaba da gudanar da ayyukan tallafawa jama’a da kyautata rayuwarsu.