Ahmed Musa da bincent Enyeama za su fafata a takarar Gwarzon dan kwallon Afirka
Hukumar kwallon kafar Afirka, CAF ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasa 37 wadanda za su yi takarar “gwarzon dan kwallon Afirka” na shekarar 2015.Yaya Toure, dan wasan tsakiya na Ibory Coast da kulob din Manchester City na Ingila, wanda shi ne ya lashe gasar a shekarar da ta gabata, ya shiga jerin ‘yan wasan […]
Hukumar kwallon kafar Afirka, CAF ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasa 37 wadanda za su yi takarar “gwarzon dan kwallon Afirka” na shekarar 2015.
Yaya Toure, dan wasan tsakiya na Ibory Coast da kulob din Manchester City na Ingila, wanda shi ne ya lashe gasar a shekarar da ta gabata, ya shiga jerin ‘yan wasan da hukumar ta fitar.
Kazalika, an fitar da sunayen Gerbinho da Mad Gradel da kuma Serge Aurier a matsayin wadanda za su yi takara.
Wasu a cikin jerin sunayen sun hada da Andrew Ayew dan Ghana na Kulob din Swansea City da Ahmed Musa dan Najeriya na kulob din CSKA Moscow; Sadio Mane dan Senegal na kulob din Southampton da Pierre-Emerick Aubameyang dan dasar Gabon, na kulob din Borussia Dortmund da bincent Enyema dan Najeriya na kulob din Lille da kuma Riyad Mahrez dan kasar Aljeriya na kulob ddin Leicester City.
Za a ci gaba da tace sunayen mutane 37 din zuwa 10 ga watan Nuwamban bana kafin a sake rage su zuwa sunaye biyar, sannan a rage zuwa ukun karshe kafin a yi bikin bayyana wanda ya lashe gasar.