Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike kan mutuwar ɗan wasan Nijeriya a Uganda
Muna buƙatar a gudanar da cikakken bincike. Kada a yi rufa-rufa ko kaɗan. Mun gano bayanai masu cin karo da juma game da rasuwarsa.

Tauraron tawagar Super Eagles Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike game da mutuwar dan wasa Abubakar Lawal wanda ake zargin ya faɗo daga wani gini ya mutu a kasar Uganda.
A jiya Litinin aka ba da rahoton mutuwar Lawal wanda ‘yan sandan Uganda suka ce ɗan wasan haifaffen Sakkwato ya mutu ne bayan ya faɗo daga benen wani katafaren kanti.
- Mayaƙan Boko Haram sun sace kwale-kwale 8 a Borno
- DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa
Cikin wani dogon saƙo da Ahmed Musa ya wallafa a shafinsa na X, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin.
“Muna baƙin ciki da samun labarin mutuwar Abubakar Lawal. Wannan lamari ne mai ban tsoro wanda akwai ayar tambayoyi da neman ƙarin haske.
“Saboda mun gano bayanai masu cin karo da juma game da rasuwarsa; Na farko an yi iƙirarin cewa hatsari ne, kuma rahoton na biyu ya ce ya faɗo daga baranda.
“Wadannan rahotannin masu cin karo da juna sun nuna wani abu ne da ke da shakku game da rasuwarsa kuma na tuntubi hukumomin Nijeriya da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) su mai da hankalinsu kan wannan mummunan lamari da ya faru a Uganda.
“Ina kira ga gwamnatin Nijeriya da Hukumar NFF da su binciki lamarin, su haɗa kai da gwamnatin Uganda domin a yi wa Lawal adalci.
“Ran Lawal ya cancanci a yi cikakken bincike kuma a yi adalci idan an samu wani da laifi.
“Allah Ya jikansa tare da bai wa iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.”
Haka kuma, sa’o’i bayan faruwar lamarin mai ban takaici, Shugabar Hukumar ’Yan Nijeriya Mazauna Ƙetare (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa ta bayyana cewar akwai “ababen zargi” game da mutuwar Lawal.
“Wannan abin takaici ne kuma kamar akwai rashin gaskiya. Muna buƙatar a gudanar da cikakken bincike. Kada a yi rufa-rufa ko kaɗan.”