Ahmed Musa ya karya farashin man fetur a Kano

Haka ma ga damar sayar da nawa.

Ahmed Musa ya karya farashin man fetur a Kano

Ahmed Musa

Fitaccen dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa, ya karya farashin man fetur a gidan mai mallakinsa da ke Jihar Kano.

Dan kwallon ya zaftare kimanin Naira 40 kan yadda galibi ake sayar da man duk lita a fadin jihar.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Ahmed ya ce ya rage farashin man fetur zuwa Naira 580 duk lita sabanin N620 da ake sayarwa a sauran gidajen mai.

A cikin sakon, fitaccen dan kwallon ya ce “yana sanar da rage farashin man fetur a gidajen mansa na MYCA7 da ke titin Zaria a Unguwa Uku daga Naira 620 zuwa 580 duk lita.”

Wani mai amfani da shafin na Twitter da sunan Scala @lakaas123, ya yi martani da cewar “Ya haka Alhaji. N580 a Kano ba ma a Legas ba. Ko dai zolaya ce kake yi mana?

Shi kuwa Musa ya mayar da martanin cewa “haka ma ga damar sayar da nawa.”

Wannan lamari dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) ya sanar da kara farashin man fetur zuwa N617 a babban birnin kasar Abuja.

Haka kuma, a daidai wannan lokaci ne aka wayi gari farashin man fetur ya koma N620 duk lita a gidajen mai na NNPCL din da ke Kano.

Ahmed Musa ya shahara a fagen sana’ar tamaula, inda a halin yanzu yake taka leda a kungiyar Sivasspor da ke bugabgasar Turkish Super Lig da kuma tawagar Super Eagles ta Najeriya.

Yau za a yi jana’izar Janar Lagbaja

NAJERIYA A YAU: Shirin Da Masu Ruwa Da Tsaki Suka Yi Kan Zaben Ondo.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025