Ahmed Musa ya koma Kano Pillars da ƙafar dama

Kano Pillars ta fara wasan cikin kuzari, inda Musa ya dauki minti hudu kacal ya fara cin kwallo.

Ahmed Musa ya koma Kano Pillars da ƙafar dama

Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya dawo gasar Premier League ta Nijeriya, inda ya zura ƙwallaye biyu yayin da Kano Pillars ta doke Sunshine Stars na Akure da ci 2-0 a ƙarshen mako.

An buga wasan ne a filin wasan da kulob din ya karɓa na wucin-gadi, inda Ahned Musa ya jagoranci ƙungiyar zuwa kaiwa ga nasara, wanda shi ne abin da ake buƙata bayan rashin nasara a wasanni biyu a jere.

A ranar Asabar aka sanar cewa Musa da mai tsaron baya na Super Eagle Abdullahi Shehu sun koma ƙungiyar ta Pillars.

Wannan shi ne wasa na biyar na gasar Firimiyar Nijeriya na kakar 2024/2025.

Wannan shi ne karo na uku da Musa yake buga wa Pillars wasa a lokuta daban-daban. Lokaci na baya-bayan nan shi ne a shekarar 2021.

Musa ya gaza samun kulob bayan da kwantiraginsa ta ƙare a watan Mayun 2024 da ƙungiyar Siɓasspor.

Kano Pillars ta fara wasan cikin kuzari, inda Musa ya dauki minti hudu kacal ya fara cin kwallo.

Musa ya karɓi ƙwallon daga Mustapha Umar kafin ya buga ƙwallo mai ƙarfi daga yadi na 18, wanda ya sa mai tsaron ragar Sunshine Stars ya gaza iya yin wani abu.

Lamarin ya ja hankalin masu bibiyar ƙwallon ƙafa, musamman masoya gasar Firimiyar Nijeriya da kuma ƙungiyar Kano Pillars ta Kano.

Da yake bayyana farin cikinsa, Ahmed Musa ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa,

na yi farin cikin dawowa Kano Pillars. Ina godiya ga dukkan ma’aikatan ƙungiyar da abokan wasana da masu horar da ’yan wasa bisa wannan damar da suka ba ni. Sannan magoya bayanmu da ma duk wadanda suka zo kallon mu.

Ya fara taka tamaula a kulob din Kano Pillars a kakar shekarar 2009 zuwa 2010, inda ya zura ƙwallo 18 a wasa 25 da ya buga, inda daga Pillars din ya bar ƙasar.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos