Ahmed Musa ya taya Kano Pillars murna

Tsohon dan kwallon Kano Pillars da yanzu haka yake kwallo a CSKA Mosko da ke Rasha Ahmed Musa a ranar Talatar da ta wuce ne ya taya kulob din Pillars murnar lashe gasar rukunin firimiya na kasa har sau uku a jere. A ranar Lahadin da ta gabata ne dai Kano Pillars ta lashe gasar […]

Ahmed Musa ya taya Kano Pillars murna
Ahmed Musa ya taya Kano Pillars murna

Tsohon dan kwallon Kano Pillars da yanzu haka yake kwallo a CSKA Mosko da ke Rasha Ahmed Musa a ranar Talatar da ta wuce ne ya taya kulob din Pillars murnar lashe gasar rukunin firimiya na kasa har sau uku a jere.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai Kano Pillars ta lashe gasar sau uku a jere bayan ta lallasa kulob din Nembe City da ci 4-0 yayin da mai biye da ita Enyimba ta yi kunnen doki da Dolphins a garin Fatakwal.
“Ina taya daukacin mahukunta kulob din Pillars da ’yan kwallon da kuma magoya bayansu murna a kan nasarar lashe gasar rukunin firimiya ta Najeriya a karo na uku a jere. A gaskiya sun cancanci yabo kuma ina alfahari da su a matsayina na tsohon dan kwallon kulob din”, inji Musa a wata takardar murna da ya aike wa kulob.
Da wannan nasara da kulob din Pillars ya samu, ya zama babu wani kulob a Najeriya bayan shi da ya taba lashe gasar ta firimiya sau uku a jere, don haka za a iya cewa a yanzu kulob din ya kafa sabon tarihi.